Sokoto na cikin jihohin da 'yan bindiga ke cin karensu babu babbaka inda suke sace mutane kuma sau tari sukan kashe su./Hoto: Rundunar Sojojin Nijeriya

Rundunar sojojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe gomman gawurtattun 'yan ta'adda a wani hari na musamman da suka kaddamar a jihar Sokoto da ke arewacin kasar.

Kakakin rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya bayyana haka a wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafukanta na sada zumunta ranar Talata.

Ya ce dakarun sojin Nijeriya sun kaddamar da "samame da aka tsara cikin nutsuwa a kauyen Tukandu don murkushe wata kungiyar gawurtattun 'yan ta'adda da ke da alhakin aikata laifuka da dama a yankin."

"Luguden wuta babu kakkautawa da dakarun suka kaddamar ya yi sanadin kawar da 'yan ta'adda da dama, yayin da wasu suka tsere da harbin bindigogi a jikinsu. Dakarun sun samu bindiga uku kirar AK-47, da bindiga daya samfurin PKT, da alburusai na musamman 125 masu tsawon 7.62 mm, da na'urorin harba rokoki guda biyu da kuma babura guda 9," in ji Birgediya Janar Nwachukwu.

Labari mai alaka: An tura sojojin sama da na kasa Zamfara bayan sace daliban Jami'ar Tarayya ta Gusau: Matawalle

A baya-bayan nan dai, rundunar sojin Nijeriya na samun nasara sosai a yakin da take yi da masu aikata laifuka a kasar.

Ko a makon jiya sai da dakarun kasar suka kashe 'yan bindiga da dama sannan suka kama akalla 73 a jihar Filato da ke arewacin kasar.

Nijeriya ta kwashe gomman shekaru tana fama da matsalar hare-haren 'yan bindiga da masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa, wadanda suka sace dubban dalibai, ciki har da na Jami'ar Tarayya da ke Gusau da ke makwabtaka da Sokoto. Kawo yanzu ba a ceto galibinsu ba, ko da yake hukumomi sun sha alwashin yin hakan.

TRT Afrika
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince