Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun kashe aƙalla ƴan ta’adda 2,352, yayin da aka kama 2,308, sannan an yi nasarar kuɓutar da mutane 1,241 da aka yi garkuwa da su a wasu mabambantan samame a faɗin ƙasar tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2024.
Kakakin rundunar tsaron ƙasar, Manjo Janar Edward Buba, ya bayyana sunayen wasu shugabannin ƴan ta’adda da aka kashe kamar su Abu Bilal Minuki wanda aka fi sani da Abubakar Mainok, da Haruna Isiya Boderi.
Buba ya ƙara da cewa dakarun sojin ƙasar sun kashe wasu daga cikin ƴan ta'addan da suke kai farmaki dajin Birnin Gwari na jihar Kaduna da kuma kan hanyar Abuja zuwa Kaduna a ranar 21 ga watan Fabrairu.
A cewar hukumomin ƙasar, hare-haren da rundunar sojin ta yi ta kaiwa ta ƙasa da sama a yankunan da ƴan ta'adda suke cin karensu babu babbaka sun taimaka wajen samun wannan nasara.
Nasarar hare-haren
''Nan-take da aka yi nasarar gano maɓoyar ƴan ta'addan, jiragen yaƙinmu suka yi ta kai hare- hare tare da harba bama-bamai a maɓoyar ƴan ta’addan,” a cewar mai magana da yawun rundunar tsaron ƙasar.
Buba ya ƙara da cewa sojojin sun kuma yi nasarar kai harin kwanton-ɓauna kan 'yan ta'adda a wasu wurare da suka addaba.
Ya ce farmakin da da rundunar sojin ta kai ya yi sanadin ƙwato makamai 2,847 da alburusai 58,492.
Kazalika mai magana da yawun rundunar ya bayyana cewa, an kai samame daban-daban kan ɓarayin ɗanyen mai, wanda ya yi sanadin ƙwato dubban litar man da aka sace.