Rundunar sojojin kasa ta Nijeriya ta ce ta karrama dakarunta 35 da kyautuka daban-daban sakamakon bajintar da suka yi “a jarrabawa daban-daban.”
Rundunar ta bayyana haka ne a wata sanarwa da mukaddashin kakakinta Laftanar Kanar Sani Uba ya wallafa a shafinsu na soshiyal midiya ranar Juma’a da maraice.
An karrama dakarun ne bayan sun samu horo sannan suka yi jarrabawa inda suka yi zarra, in ji sanarwar.
Mai magana da yawun rundunar sojin ya ce wadanda aka karrama “dakaru ne da suka yi nasara a jarrabawa daban-daban da Rundunar da ke ba da HAoro ta Training and Doctrine Command” ta gudanar a karkashin rundunar sojin kasa.
An ba su horon ne a Minna, babban birnin jihar Neja ranar Talatar da ta gabata inda shugaban sashen bayar da horo na rundunar sojin kasa ta Nijeriya Manjo Janar SG Mohammed ya wakilci shugaban sojojin kasa Laftanar Janar TA Lagbaja, a cewar sanarwar.
A yayin da yake jawabi, Kwamandan rundunar da ke bayar da horo ta TRADOC, Manjo Janar Kevin Aligbe ya ce an kaddamar da kyautukan ne domin saka wa wadanda suka yi "zarra" abin da ya bayyana a matsayin ginshiki na samun nasara.
A sakon da aka gabatar a madadin Laftanar Janar TA Lagbaja, an ambato shi yana gode wa rundunar da ke bayar da horon bisa jajircewarta wajen samar da nagartattun sojoji ta hanyar horo mai inganci.