Rundunar sojin Nijeriya ta ce za ta ci gaba da zama a yankin Okuama sai ta gano mutanen da suka kashe  jami'anta 17

Rundunar sojin Nijeriya ta ce za ta ci gaba da zama a yankin Okuama sai ta gano mutanen da suka kashe  jami'anta 17

Manjo Janar Abdussalam ya jaddada cewa babu "wata farfaganda da bi-ta-da-ƙulli da ƙarairayi da za su janye hankalin dakarun daga cim ma manufofin da suka sanya a gaba".
Shugaba Tinubu ya ce nan ba da jimawa ba za a yi wa sojojin jana'izar ban-girma tare da karrama su da lambobin yabo na ƙasa./Hoto: Rundunar Sojojin Nijeriya

Rundunar sojojin ƙasa ta Nijeriya ta ce dakarunta ba za su fice daga yankin na Jihar Delta ba sai an "gano" mutanen da suka yi wa jami'anta goma sha bakwai kisan gilla a makon jiya.

Kwamandan Runduna ta Shida da ke ƙarƙashin rundunar ko-ta-kwana a Kudu Maso Kudancin Nijeriya, Manjo Janar Jamal Abdussalam ne ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da shugaban hukumar raya yankin Neja-Delta Samuel Ogbuku ya ziyarce a Fatakwal.

Sanarwar da rundunar sojin ta Nijeriya ta fitar ta ambato Manjo Janar Abdussalam yana cewa Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya ba su umarnin "gano makaman da waɗanda suka aikata wannan ɗanyen-aiki suka ƙwace tare da tabbatar da ganin an kama dukkan masu hannu a lamarin."

Ya ƙara da cewa dakarunsu za su "ci gaba da zama a surƙuƙin (yankin Neja-Delta) har sai an cim ma waɗannan manufofi."

Manjo Janar Abdussalam ya jaddada cewa babu "wata farfaganda da bi-ta-da-ƙulli da ƙarairayi da za su janye hankalin dakarun daga cim ma manufofin da suka sanya a gaba".

A ranar Alhamis ɗin makon jiya ne wasu ɓata-gari a ƙauyen Okuama na Jihar Delta suka kashe sojojin Nijeriya goma sha bakwai lokacin da suka je ƙauyen domin kai wa mutane ɗauki sakamakon rikicin ƙabilanci.

Sojojin sun haɗa da kwamanda ɗaya da masu muƙamin manjo guda biyu da kyaftin ɗaya da kuma ƙananan sojoji 13.

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bayyana matuƙar ɓacin ransa kan lamarin waɗanda ya ce ce "matsorata" ne suka aikata shi, yana mai bai wa Hedkwatar Tsaro da shugaban rundunar tsaron Nijeriya "cikakken iko" su hukunta duk wanda aka samu da laifi da hannu a kisan.

Kazalika ya ce nan ba da jimawa ba za a yi wa sojojin jana'izar ban-girma tare da karrama su da lambobin yabo na ƙasa.

TRT Afrika