Rundunar sojin ta Nijar ta ce soja ɗaya ya rasa ransa a wannan farmakin . / Hoto: Reuters

Rundunar sojin Nijar ta ce ta yi nasarar kashe ƴan ta'adda da dama sakamakon farmakin da ta kai musu a Kogin Isa da Kogin Kwara.

A sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce daga waɗannan yankunan ne ƴan ta'addan ke kitsa jerin hare-haren da suka zafafa kai wa yankin a baya-bayan nan, lamarin da ya fara zama barazana ga birnin Yamai da kewayensa.

Wannan farmakin da rundunar sojin Nijar ta ƙaddamar ta sama da kuma ƙasa ta ce ya ba ta damar kashe ‘yan ta'adda kusan 60 a yakin Kolo Kolo na jihar Tillaberi, sannan ta jikkata da dama daga cikin ƴan ta'addan.

Baya ga haka rundunar sojin ta ce ta kuma kama wasu tare da tarwatsa wasu abubuwa masu fashewa kusan 30, da kama wasu tarin babura da makamai da harsasai da wasu na'urori na sadarwa na ƴan ta'addan.

Rundunar sojin ta Nijar ta ce soja ɗaya ya rasa ransa a wannan farmakin yayin da motar sojoji ɗaya ta lalace bayan ta taka nakiya.

Ta ce a yanzu haka tana ci gaba da aiwatar da wani aikin na samame a jihar Maradi da yankin Tawa, inda a can din ma sojojin suka yi nasarar kashe ƴan ta'adda da dama da kuma wasu tsageru.

Sannan a yankin Diffa ma ta yi nasarar kama wasu motoci dauke da kayan abinci da wasu kayan ƙera jiragen kwale-kwale "da za a kai wa ƴan ta'addar Boko Haram" a wannan yanki.

TRT Afrika