Rundunar sojin kasa ta Nijeriya ta ce ita ce ta yi kuskuren kai hari kan rukunin masu Maulidi a Kaduna.
Tun da farko Rundunar Sojin Saman kasar ta fitar da sanarwa inda ta ce ba ita ta kai hari kansu ba tare da jaddada cewa ba ita kadai ke amfani da jiragen yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba.
Da safiyar Litinin ne wasu daga cikin kafafen watsa labaran Nijeriya suka rika ruwaito cewa jirgin sama wanda ake zargin na sojojin saman Nijeriya ne ya kai hari a Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.
Lamarin ya faru ne da misalin karfe 9:00 na dare a ranar Lahadi.
A sanarwar da gwamnatin Jihar Kaduna ta fitar ranar Litinin ta ce rundunar sojin ce ta bayyana mata yadda lamarin ya kasance, a wani taro da ya samu halartar hukumomin tsaro da malaman addini da sarakuna.
"Babban janar din da ke kula da rundunar sojin a wannan shiyyar Major VU Okoro ya bayyana cewa rundunar sojin tana wani aiki ne da ta saba yi a kan ƴan ta'adda amma a bisa kuskure sai abin ya shafi al'ummar yankin.
"Ana ci gaba da aikin ceto a wajen da lamarin ya faru, yayin da tuni aka kwashe wasu da suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Barau Dikko," a cewar sanarwar Ma'aikatar Tsaron Cikin Gida ta Jihar Kaduna.
Musanta labarin da rundunar sojin sama
“Labaran da ke yawo wanda ake zargin Rundunar Sojin Saman Nijeriya ta kai hari bisa kuskure kan farar hula a Kaduna ba gaskiya ba ne,” kamar yadda mai magana da yawun sojin saman Nijeriya Edward Gabkwet ya sanar tun da fari.
“Akwai bukatar a san cewa sojojin sama ba su kai wani samame a Kaduna a sa’o’i 24 da suka gabata ba. Haka kuma akwai bukatar a san cewa ba Rundunar Sojin Saman Nijeriya ce kadai ke amfani da jirage marasa matuka na yaki a Arewa Maso Yammacin Nijeriya ba,” in ji sanarwar.