Rikicin DRC: Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula sun tsere zuwa Rwanda

Rikicin DRC: Jami'an Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula sun tsere zuwa Rwanda

'Yan tawayen M23 sun yi iƙirarin ƙwace birnin Goma mai muhimmanci a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo.
Jami'an bayar da agaji sun tsere daga Goma sannan dubban fararen hula su ma sun tsere. / Hoto: Reuters

Ɗaruruwan ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da fararen hula a gabashin Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo sun tsere zuwa maƙociyar ƙasar, Rwanda, yayin da gomman sojojin Kongo ɗin suka “miƙa wuya” ga jami’an tsaron Rwanda a ranar Litinin, bayan ‘yan tawayen M23 sun ƙwace iko da birnin Goma mai muhimmanci a Kongo.

Wasu bidiyoyi da gidan Radiyo da Talabijin na Rwanda ya wallafa a shafin X, sun nuna wani abin da ke nuna kamar sojoji ne, wasu cikin kayan sarki, suna miƙa makamai ga jami’an tsaron Rwanda, bayan tsallakawa gabashin ƙasar mai maƙotaka ta kan babbar iyakar ƙasar a yankin Rubavu na Rwanda.

Lamarin na baya-bayan nan ya zo ne sa’o’i bayan ‘yan tawayen M23 sun yi iƙirarin shiga Goma, abin da ya tilatsa wa mutane tsarewa daga birnin.

‘Yan tawayen na M23, waɗanda ake zargin suna samun goyon bayan Rwanda, sun zafafa hare-hare a gabashin Kongo a makon jiya, inda suka ƙwace muhimman birane.

Sai dai Shugaban Rwanda Paul Kagame ya sha musanta zargin cewa yana goyon bayan ‘yan tawayen.

Mummunan fasa gidan yari a Goma

An fuskanci wani gagarumin fasa gidan yari da safiyar Litinin a birnin Goma na Kongo da aka yi wa kofar-rago, sa’o’i bayan mayaƙa daga ƙungiyar ‘yan tawayen ta M23 sun shiga birnin, kamar yadda wasu majiyoyi suka shaida wa AFP.

An yi wa gidan yarin wanda yake da fursunoni kimanin 3,000 raga-raga, bayan ɓalla gidan yarin, abin da ya haifar da “mace-mace”, a cewar majiyoyin, ba tare da bayar da wani ƙarin bayani ba.

Ana iya ganin fursounonin da suke tserewa a titunan da suke kusa da yankin, kamar yadda wani wakilin AFP ya bayyana.

Shugabannin ƙasashen Gabashin Afirka za su yi taron gaggawa

Shugaban Kenya William Ruto, wanda yake shugabancin Ƙasashen Gabashin Afirka ya sanar a ranar Lahadi cewa, ƙungiyar za ta gudanar da wani taro na musamman a cikin sa’o’i 48 don tunkarar rikicin da yake yaɗuwa a Jamhuriyar Dimukuraɗiyar Kongo.

Ruto ya tabbatar da cewa tun da farko ya tattauna da Shugaban DRC Kongo Felix Tshisekedi da Shugaban Rwanda Paul Kagame, waɗanda dukkansu suka amince za su halarci taron.

A wata sanarwa da ofishin shugaban ƙasa ya fitar a Kenya, Ruto ya bayyana damuwa kan yadda lamarin yake ƙara taɓarɓarewa a yankin, abin da ya haifar da mummunan yanayi da kuma jefa jama’a cikin mawuyacin hali.

Ya ce rikicin a Kongo ya haifar da munanan ayyukan soja, da rufe filin jirgin sama na Goma, abin da ya ƙara jefa jama’ar yankin cikin mawuyacin hali.

An rufe iyakar DRC da Rwanda

An rufa iyakar Rwanda da DRC kusa da birnin Goma da aka yi wa ƙofar-rago a ranar Litinin, a cewar shaidu, ‘yan sa’o’i bayan ‘yan tawaye sun shiga babban birnin ƙasar Kongo da ke Gabashin Afirka.

“Babu mai shiga babu mai fita, in ban da tsirarun ma’aikatan Majalisar Ɗinkin Duniya da iyalensu da suka fice da safen nan,” kamar yadda wani ma’aikacin agaji a kan iyakar ƙasashen biyu ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.

Harbe-harbe a Goma

Mazauna birnin Goma mafi girma a gabashin ƙasar, sun wayi garin Litinin suna fargaba da zaman rashin tabbas kan wanda ke da iko da yankin, bayan ‘yan tawayen da ke samun goyon bayan Rwanda sun yi zargin cewa sun ƙwace birnin, yayin da rikicin da suke yi da jami’an tsaron Kongo ya faɗaɗa a cikin ‘yan kwanakin nan a rikicin da ya fi kowanne daɗewa a Afirka.

An riƙa jin ƙarara harbe-harbe a duka faɗin Goma a cikin dare kafin a ga gomman mutane sanye da kayan sojoji da sanyin safiyar Lahadi suna tunkarar birnin da bindigoginsu, wanda shi ne babban birnin yankin Kivu.

Babu tabbas idan mutanen — waɗanda wasu mazauna birnin suke riƙa yi wa jinjina daga gefen hanya — ‘yan tawayen M23 ne. Gwamnatin Kongo ba ta tabbatar da rahotannin ƙwace birnin ba.

Rwanda ‘a shirye take’ a samu zaman lafiya

Rwanda ta sanar a ranar Lahadi cewa a ko da yaushe a shirye take a bi hanyar siyasa a rikicin na gabashin Jamhuriyyar Dimukuraɗiyyar Kongo, inda ‘yan tawayen M23 suke yaƙi da dakarun gwamnati.

Mummunan yaƙin na baya-bayan nan a birnin Goma, wanda shi ne babban birnin yankin, ya faro ne bayan yawan saɓa yarjejeniyar tsagaita wuta da sojojin Kongo da sojojinta na ƙawance, a cewar Ma’aiakatar Harkokin Waje a ciki wata sanarwa.

Ta sanar da cewa yaƙin da ake yi a kusa da iyakar Rwanda ya ci gaba da zama wata gagarumar bazarana ga tsaron Rwanda da ‘yancin ƙasar, abin da ya sa ta ɗauki matakin kare ƙasarta.

Rwanda ta bayyana damuwa kan rashin wani muhimmin batu a cikin sanarwar da ɓangarori daban-daban da ke da hannu a rikicin a gabashin Jamhuriyyar Dimukuraɗiyyar Kongo. Kalaman da ba su kamata ba, ko kuma kalaman juya tunanin mutane ba za su haifar da wani kyakkyawan sakamako ba.”

Yayin wani taron gaggawa na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya a ranar Lahadi, DRC Kongo ta nemi Rwanda ta janye dakarunta daga Kongo nan-take, ta kuma nemi a sanya takunkumai kan jami’an Rwanda da aka same su da hannu a rikicin.

TRT Afrika