Rikicin ƙabilanci tsakanin al'ummomi biyu a gabashin Chadi ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 42. Hoto: AP

Rikicin ƙabilanci tsakanin al'ummomi biyu a gabashin Chadi ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 42, a yankin ƙasar da ke yawan fama da rikice-rikice a kan gonaki, a cewar Ma'aikatar Tsaro.

Ma'aikatar ba ta faɗi wadanda ke da hannu a rikicin ba ko kuma tsawon lokacin da aka ɗauka ana yi, amma ana yawan samun rikici a yankin tsakanin manoma da makiyaya ko wasu ƙungiyoyin, duk a kan filaye.

A cikin sanarwar da ta fitar, ma'aikatar ta ce an kama mutum 175 a wajen da aka yi faɗan, inda wasu masu ɗauke da makamai suka cinna wa wani babban yanki na ƙauyen Tileguey a gundumar Ouaddai wuta.

"An shawo kan lamarin amma ina ƙoƙarin sasanta ɓangarorin," kamar yadda Ministan Tsaro Janar Mahamat Charfadine Margui ya shaida wa AFP.

Ministan ya je wajen da aka yi rikicin, inda ya jagoranci wata tawagar gwamnati da sojojin da za su "bayar da cikakkun bayanai" a kan lamarin.

Ana yawan samun rikice a gabashi da kudancin Chadi, inda mazauna yankin da dama ke ɗauke da malamai, sakamakon yadda manoma ke zargin makiyaya da barin dabbobinsu suna cinye musu kayan amfanin gona.

AP