Ana ci gaba da musayar wuta a Khartoum babban birnin Sudan inda rundunar RSF ta kara kai hari hedikwatar sojin kasar kwana biyu a jere.
An shafe sama da wata biyar ana rikici tsakanin sojin Sudan da rundunar RSF, lamarin da ya jawo asarar dubban rayuka.
“Ana musayar wuta a yanzu kusa da hedikwatar soji da makamai daban-daban,” kamar yadda wani ganau ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP a ranar Lahadi daga Khartoum.
Wasu mutanen kuma sun bayar da rahoton rikicin da ake gwabzawa a birnin El-Obeid mai nisan kilomita 350 daga Khartoum.
Rikici tsakanin RSF da sojojin na Sudan ya kara kamari a ranar Lahadi, inda aka kona gine-gine da dama da ke tsakiyar Khartoum.
A wasu sakonni da aka wallafa a shafukan sada zumunta wadanda kamfanin dillancin labarai na AFP ya tantance, mutane sun ta yada bidiyon yadda wuta ke ci bal-bal a wasu yankuna na Khartoum, daga ciki har da wani dogon ginin kamfanin mai na Greater Nile.
Masu amfani da kafofin sada zumunta sun rinka nuna rashin jin dadinsu kan yadda Khartoum ta zama. Wani bidiyo da aka wallafa ya nuna yadda tagogin wani gidan sama da ake daukar bidiyon a cikinsa suka tarwatse da kuma yadda gidajen da ke makwaftaka suka sha ruwan harsasai.
Mutuwar mutum 7,500
Tun bayan barkewar yaki a Sudan a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin shugaban sojojin na Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo, kusan mutum 7,500 aka yi kiyasin cewa an kashe.
Haka kuma wannan yakin ya sa sama da mutum miliyan biyar sun rasa muhallansu, daga ciki har da mutum miliyan 2.8 wadanda suka tsrere saboda hare-hare ta sama da ake ci gaba da kaiwa, da harbe-harben makaman atilari.
Miliyoyin mutanen da suka rage a birnin sun wayi garin Lahadi inda suka ga sararin samaniya ya turnuke da hayaki inda kuma suke ci gaba da jin karar harbe-harben bindiga a fadin birnin.
“Muna iya jin kara sosai,” kamar yadda wani da ya shaida lamarin ya shaida wa AFP a ranar Lahadi daga gundumar Mayo da ke kudancin Khartoum inda a nan ne rundunar ta RSF take kai hari ga sansanonin soji da makaman atilari.