Rebecca Cheptegei: 'Yar wasan tsere ta Uganda ta mutu bayan saurayinta ya cinna mata wuta a Kenya

Rebecca Cheptegei: 'Yar wasan tsere ta Uganda ta mutu bayan saurayinta ya cinna mata wuta a Kenya

Bayanai sun ce 'yar wasan tseren Uganda Rebecca Cheptegei ta mutu ne bayan saurayinta ya watsa mata fetur sannan ya cinna mata wuta a Kenya.
Rebecca Cheptegei  Photo : TRT Afrika

'Yar Uganda da ke wasan tsere a gasar Olympic Rebecca Cheptegei ta mutu bayan saurayinta ya cinna mata wuta a ƙasar Kenya, a cewar shugaban kwamitin gasar Olympic na ƙasar Uganda ranar Alhamis.

"Mun samu labari mai cike da baƙin-ciki na mutuwar ɗaya daga cikin 'yan wasan tserenmu na gasar Olympic Rebecca Cheptegei...bayan saurayinta ya kai mata hari," in ji Donald Rukare a saƙon da ya wallafa a shafin X.

'Yar wasan tseren ta Uganda ta mutu ne kwana biyu bayan jami'ai sun ce an garzaya da ita sashen bayar da kulawar gaggawa na wani asibiti a Kenya.

Hukumomi sun ce saurayinta ne ya watsa mata fetur ranar Talata bayan sun yi faɗa sannan ya cinna mata wuta.

Bayanai daga 'yan sanda sun ce saurayin Rebecca Cheptegei, 'yar shekara 33, mai suna Dickson Ndiema Marangach ya shiga ɗakinta a garinsu Endebess da ke yankin Trans-Nzoia na ƙasar Kenya da misalin ƙarfe biyu na rana a Lahadin da ta gabata yayin da ita da 'ya'yanta suke coci.

"Dickson, wanda ke riƙe da galan cike da fetur, ya watsa wa Rebecca sannan ya cinna mata wuta," a cewar 'yan sanda, suna masu ƙarawa da cea shi ma ya samu raunuka sakamakon wutar da ta ƙona shi.

Reuters
Muna amfani da ka’idojin yanar gizo. Muna son ku san cewa idan kuka ci gaba da amfani da wannan shafin, kun amince da wadannan ka’idojin.Ka’idoji
Na amince