Gwamnatin Burkina Faso ta ce ta sanya hannu kan yarjejeniyar gina tashar makamashin nukiliya da Rasha domin "biyan bukatarmu ta samar da makamashi ga jama'armu."
Kasa da kashi daya cikin hudu na 'yan kasar ne suke samun hasken lantarki.
"Gwamnatin Burkina Faso ta sanya hannu kan yarjejeniyar gina tashar makamashin nukiliya," in ji sanarwar da gwamnatin sojin kasar ta fitar ranar Juma'a.
A watan Yuli ne shugaban mulkin sojin Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya nemi taimakon shugaban Rasha Vladimir Putin domin ya gina tashar makamashin nukiliya a Ouagadougou.
TRT Afrika