Ministan Ayyukan Gona na Rasha ya ce Moscow ta fara aika hatsi tan 200,000 kyauta zuwa ƙasashen Afirka, kamar yadda Shugaba Vladimir Putin ya yi alkawari a watan Yuli.
Tuni dai jiragen ruwa da suka nufi Burkina Faso da Somaliya suka bar tasoshin jiragen ruwa na Rasha, kuma nan ba da jimawa ba za a ƙara jigilar wasu zuwa kasashen Eritrea da Zimbabwe da Mali da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, in ji Dmitry Patrushev a wata sanarwa da aka wallafa a kafar Telegram a ranar Juma'a.
Putin ya yi alkawarin isar da hatsi kyauta ga kasashen shida a wani taro da ya yi da shugabannin Afirka a watan Yuli, jim kadan bayan Moscow ta janye daga yarjejeniyar da ta bai wa Ukraine damar jigilar hatsi daga tashar ruwan Tekun Bahar Aswad duk da yaƙin na Rasha.
Miliyoyin tan na hatsi
Yarjejeniyar da aka fi sani da shirin hatsi na Bahar Aswad da Turkiyya ta kulla, ta taimaka wajen rage farashi a kasuwannin duniya inda kasashen Afirka ke cin moriya.
A karkashin yarjejeniyar da aka cimma, an yi jigilar sama da tan miliyan 33 na hatsi daga tasoshin jiragen ruwa na Ukraine, lamarin da ya hana fuskantar matsalar abinci a duniya.
A bara, Rasha ta fitar da kusan tan miliyan 60 na hatsi, a cewar Putin. Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya kira alkawuran fitar da hatsin kyauta da "wani ɗan taimako da ba zai isa ba", kamar yadda Reuters ta rawaito.
Tun bayan matakin da Rasha ta ɗauka na janyewa daga shirin, ake ta samun matsaloli wajen fitar da hatsi daga tasoshin jiragen ruwan Ukraine da Rasha.
Sai dai Ukraine ta fada a ranar Juma'a cewa ta yi nasarar jigilar kaya na tan miliyan 4.4 da suka hada da tan miliyan 3.2 na hatsi ta wata sabuwar hanyar jigilar kayayyaki da ta kafa a watan Agusta.