Fitaccen mawakin siyasar nan na Nijeriya, Dauda Kahutu Rarara, ya ce ya soma biyan ‘yan sandan nan uku da aka kora daga aiki albashinsu.
A wani bidiyo da mawakin ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa a ranar 30 ga wata ya tura wa kowa albashinsa.
“Su ma’aikatana da aka kora, na dauki nauyin zan ci gaba da biyansu albashi iya yadda ake biyansu, kuma Alhamdulillahi yau ne 30 ga wata, na tura wa kowa albashin shi,” in ji mawakin.
Mawakin ya kara da cewa har ya mutu zai ci gaba da biyansu albashin da aka saba biyansu.
A watan da ya gabata ne rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta kori wasu ‘yan sanda uku wadanda suke bai wa Rarara kariya bisa samunsu da laifin saba ka’idar aiki.
Jami’an uku da aka sallama sun hada da Insifekta Dahiru Shuaibu da Sajan Abdullahi Badamasi da kuma Isah Danladi.
Me ya sa aka sallami ‘yan sandan?
A kwanakin baya ne wani bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna ‘yan sandan uku suna harba bindiga a sama a garin Kahutu yayin da suke yi wa mawakin rakiya.
A nasa bangaren, Dauda Kahutu Rarara ya bayyana cewa 'yan sandan sun yi harbi ne bayan da suka samu labarin cewa wasu bata-gari za su tayar da tarzoma yana mai cewa ba don nishadi suka yi harbi a iska ba.
“Mun je muna rabon abinci a Kahutu, sai wasu bata-gari suka shigo suna neman su tayar da tarzoma, a nan wurin ne muka samu matsala ‘yan sandanmu suka yi harbi sama,” a cewar Rarara.
Sai dai daga baya rundunar ‘yan sandan kasar ta sallami jami’an uku sakamakon samunsu da laifukan da suka hada da amfani da bindiga ba bisa ka'ida ba da wuce gona da iri da rashin da'a da kuma bata harsashin gaske.
"Wannan lamari ba mugun laifi da rashin kwarewa kawai yake nunawa ba, har da jawo wa rundunar da ma kasa baki daya abin kunya," in ji rundunar 'yan sandan a sanarwar da ta fitar bayan sallamar jami'an nata.