Kwamitin ganin wata na Mai Alfarma Sarkin Musulman Nijeriya ya ayyana Litinin a matsayin ranar daya ga watan Zul-Hajjah ta shekarar 1444 bayan Hijira.
Ranar ta yi daidai da 19 ga watan Yunin shekarar 2023.
Wata sanarwa da kwamitin ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi ta ambato Sarkin Musulman Nijeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar, na cewa Laraba 28 ga watan Yuni ita ce ranar Babbar Sallah.
Sarkin Musulmi ya taya al'umma murnar shiga watan Babbar Sallar yana mai fatan za a yi bukukuwan Sallah lafiya, in ji sanarwar.
A gefe guda, majalisar Musulman Saudiyya ta ayyana 27 ga watan Yuni a matsayin ranar Arafat tana mai cewa 19 ga watan Yuni ce daya ga watan Zul-Hajjah.
Wata sanarwa da shafin intanet na Haramain ya wallafa ce ta bayyana hakan.
TRT Afrika