Ana sa ran Shugaba Cyril Ramaphosa zai yi jawabi ga dandazon magoya baya. / Hoto: AP

Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya ce Jam’iyyar ANC za ta yi aiki tuƙuru domin samar da ayyukan yi a daidai lokacin da da rashin aikin yi ke ƙaruwa a ƙasar.

Ramaphosa ya bayyana haka ne a filin wasa na Moses Mabhida a ranar Asabar a lokacin da yake jawabi domin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen jam’iyyarsa a babban zaɓen da za a gudanar na ƙasar a watan Mayu

Ana sa shi ma Jacob Zuma wanda abokin adawar Ramaphosa ne kuma tsohon shugaban ƙasar zai gabatar da jawabi a lardin KwaZulu-Natal, wanda muhimmin yanki ne ga zaɓen ƙasar.

Jam'iyyar ANC wadda ke kan mulki a ƙasar tun 1994 bayan shigowar dimokuraɗiyya, a halin yanzu tana fama da ƙarancin goyon baya inda kuma ake yi mata zargin cin hanci da rashawa.

Tasirin Zuma

Sakamakon ya jima yana jin haushin yadda aka tilasta masa sauka daga kan muƙaminsa na shugaban ƙasa, tsohon shugaban ya shiga wata jam'iyya ta adawa domin ƙoƙarin rage wa ANC ƙuri'u.

"Zuma shi ne babbar barazana ga ANC a KwaZulu-Natal," in ji Zakhele Ndlovu, wanda malamin siyasa ne a Jam'iar KwaZulu-Natal da ke Durban.

Rikicin da ke tsakanin shugabannin biyu zai fito fili ne a ranar Asabar, lokacin da jam’iyyar ANC ke sa ran magoya baya 85,000 za su cika filin wasan kwallon kafa a birnin Durban domin kaddamar da shirinta na zaben.

Yiwuwar haɗaka

Lardi na biyu wanda ya fi yin suna a Afirka ta Kudu shi ne KwaZulu-Natal wanda ake kallonsa a matsayin wani zakaran gwajin dafi dangane da nasarar ANC a zaɓen.

Lardin ne ke da mambobi ƴan ANC mafi yawa sai dai a halin yanzu jam'iyyar na cikin matsi sakamakon haɗaka da aka yi tsakanin Democratic Alliance da ƙawarta nkatha Freedom Party.

"Idan ANC ba ta taka rawar a zo a gani a KwaZulu-Natal ba, ba za ta samu nasara a ƙasa ba," in ji Susan Booysen, wanda wani mai sharhi ne kan siyasa ga cibiyar Mapungubwe Institute for Strategic Reflection..

Ƙuri'ar jin ra'ayi ta nuna cewa jam'iyyar za ta iya samun aƙalla kaso 40 cikin 100 na ƙuri'un ƙasar, wanda hakan zai iya tilasta mata ta buƙaci gwamnatin haɗaka ta ci gaba da mulki.

Sai dai sakamakon matsaloli na kasafin kuɗi, ba lallai ne Ramaphosa ya yi manyan alƙawura na zaɓe ba.

AFP