Ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen kudancin Afirka (SADC) da kuma ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen gabashin Afirka (EAC) sun naɗa tsofaffin shugabannin ƙasashe, Uhuru Kenyatta na Kenya da Olusegun Obasanjo na Nijeriya da kuma tsohon Firaiminista Hailemariam Desalegn na Ethiopia a matsayin masu shiga tsakani wajen tsara shirin samar da zaman lafiya a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.
An ɗaiki wannan mataki ne bayan wani taro na musamman da shugabannin ƙasashen EAC da SADC suka yi a Dar es Salaam na Tanzania a farkon wannan watan domin kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, inda ‘yan tawayen M23 suke gwabza faɗa da dakarun gwamnati.
"An buƙaci dukkan ɓangarorin su mutunta tsagaita wutar da aka ayyana a taron EAC da SADC, kuma an yi kira ga M23 da kuma sauran ɓangarorin su dakatar da kutsawa cikin gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo tare da mutunta tsagaita wuta," in ji ƙungiyoyin a wata sanarwar da suka fitar.
Yaƙi a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo ya yi sanadiyyar mutuwar mutum fiye da 7,000 a wannan shekarar, kamar yadda Firaiministar ƙasar Judith Suminwa Tuluka ta shaida wa kwamitin kare haƙƙin ɗan'adam na Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Litinin.
Ƙungiyar ‘yan tawayen ta ƙarfafa ikonta a gabashin ƙasar tun watan Disamba inda ta ƙwace iko da manyan biranen lardunan Goma da Bukavu.