Ko a watan Satumbar bara sai da hukumar birnin tarayyar ta ƙwace filaye da dama a sassa daban-daban na birnin saboda ƙin mayar da hankali wurin gina su. / Hoto: FCTA

Ministan Abuja Nyesom Wike ya soke izinin mallakar filaye 568 a Abuja babban birnin ƙasar.

Hukumar gudanarwa ta Abuja ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sunayen mutum 568 da kuma lambobin filayensu da ta ƙwace.

Hukumar ta ce ta ƙwace iko da filayen ne sakamakon ƙin biyan kuɗin takardar shaidar mallakar fili da mamallaka filayen ba su yi ba. Filayen da aka ƙwace izinin mallakarsu na a unguwannin Maitama II da Cadastral Zone A10, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar ta ce an ƙwace izinin mallakar filayen ne, “bisa tanadin sashe na 28 na dokar amfani da filaye na shekarar 1978 kan saɓa wa ƙa’idojin bayar da izini wadda ta buƙaci masu filayen su biya kuɗaɗen da ake bin su. Duk da haka, ana jan hankalin masu filaye waɗanda suka kammala biyan kuɗinsu a ranar ko kuma kafin 15/01/2025 kan cewa wannan bai shafe su ba,” kamar yadda sanarwar ta tabbatar.

Tun bayan zamansa ministan Abuja, Nyesom Wike ya fito da sabbin tsare-tsare a birnin daga ciki har da tilasta wa mazauna birnin waɗanda ba su da takardun shaidar mallakar fili biyan kuɗi domin su samu takardar izinin.

Ko a watan Satumbar bara sai da hukumar birnin tarayyar ta ƙwace filaye da dama a sassa daban-daban na birnin saboda ƙin mayar da hankali wurin gina su.

TRT Afrika