Nuhu Ribadu

Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Tsaro, NSA, Nuhu Ribadu ya tabbatar wa al’ummar jihohin Kogi da Bayelsa da Imo cewa an samar da cikakken tsaro a zaɓukan da za a yi a gobe Asabar a jihohin.

Ya yi gargadi ga masu ruwa da tsaki a siyasa da su guji tayar da rikici, tare da jan hankalin hukumomin tsaro da su tabbatar da bin doka da tsari a yayin gudanar da zaɓukan.

A gobe Asabar ne za a gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohin uku, waɗanda duk za su zama masu zafi kamar yadda masu sharhi ke cewa.

“NSA na ba da tabbacin cewa hukumomin tsaro sun shirya tsaf bisa umarnin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, don tabbatar da tsaro da kuma ganin an gudanar da sahihan zaɓuka a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamban 2023,” a cewar sanarwar da shugaban sashen sadarwa na ofishin Nuhu Ribadun, Zakari U. Mijinyawa ya fitar a ranar Juma’a.

NSA, wanda yana kuma daga cikin Shugabannin Kwamitin Tuntuba tsakanin Hukumomin Tsaro kan Zaben, ya tuhumi dukkan hukumomi da jami’an tsaro da na leken asiri da aka tura don yin aikin tsaro a zaben da su gudanar da ayyukansu cikin tsari.

“Gwamnatin Tarayya ta samar da duk wasu abubuwa da ake buƙata don aiwatar da zabukan cikin tsari, tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki a zabukan da su bi umarnin da Shugaban Kasa ya bayar sau da ƙafa.”

Nuhu Ribadu ya kuma yi gargadin cewa an girke na’urorin da za su sa ido sosai a wuraren zaɓukan don tattaro duk wasu shaidu na rikici da kuma aikata ba daidai ba.

Ya kuma sha alwashin cewa duk wanda aka kama da jawo hargitsi a wajen zaɓukan zai fuskanci hukunci.

Sannan ya shawarci masu kada kuri’a a jihohin uku da su fito ƙwansu da ƙwarƙwata domin gudanar da zabe, inda ya ba su tabbacin samun cikakkiyar kariya.

TRT Afrika