A ranar Lahadi 15 ga Satumba aka soma lodin kashi na farko na man fetur daga matatar mai ta Dangote da ke Legas. / Hoto: Reuters

Kamfanin mai na Nijeriya NNPCL ya fitar da sabon farashin da za a rinƙa sayar da man fetur a ƙasar bayan ya fara karɓar fetur ɗin daga matatar Dangote a ranar Lahadi.

Kamfanin ya sanar da farashin ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin da safe.

NNPCL ɗin ya bayyana cewa a Jihar Borno da kewaye za a sayar da fetur ɗin har kan N1,019 kan kowace lita sai kuma Kaduna da Sokoto da Kano da wasu jihohin za a sayar da fetur ɗin kan N999.22.

Sai kuma Abuja babban birnin ƙasar za a sayar da fetur ɗin kan 992.2

Sai kuma jihar 0yo kan N960 sai Ribas 980 kan N960 kan kowace lita.

A cewar NNPCL, a Jihar Legas ne za a fi sayar da fetur ɗin a farashi mai rahusa inda za a rinƙa sayar da shi kan N950.22 kan kowace lita.

Kamfanin na NNPCL ya tabbatar da cewa a wannan watan na Satumba zai biya kamfanin Dangote da dala domin ɗaukar man fetur, inda ya ce a ranar 1 ga watan Oktoba ne zai soma biya da naira.

Kamfanin na NNPC ya bayar da tabbacin cewa idan aka samu sabani game da farashin da aka yanke, za yi matuƙar godiya ga duk wani rangwamen da matatar Dangote za ta yi, wanda rangwamen zai je ga jama’a kai tsaye.

TRT Afrika