Gwamnatin Nijeriya ta tabbatar da cewa a ranar Lahadi 15 ga Satumba za a soma lodin kashi na farko na man fetur daga matatar mai ta Dangote da ke Legas.
Kwamitin shugaban Nijeriya kan sayar da ɗanyen mai ne ya sanar da hakan a ranar Juma’a a Abuja.
Shugaban hukumar tattara haraji ta Nijeriya Zach Adedeji wanda mamba ne a kwamitin ya bayyana cewa daga ranar 1 ga watan Oktoba, kamfanin na NNPCL zai soma bayar da ganga 385 ta ɗanyen mai a kullum ga matatar Dangote.
Ya ƙara da cewa ita kuma matatar ta Dangote za ta bayar da fetur da man dizel wanda ya zo daidai da darajar man a kasuwa kuma a biya kuɗin a naira.
An shafe lokaci ana kwan-gaba kwan-baya tsakanin kamfanin na NNPCL da kuma matatar ta Dangote dangane da batun ciniki da hada-hada ta ɗanyen mai.
Haka kuma duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka samu ƙarin kuɗin mai a Nijeriya, lamarin da ya ƙara saka ‘yan ƙasar da dama ƙorafi.
A farkon watan nan ne aka wayi gari gidajen mai mallakar kamfanin na NNPCL sun ƙara farashin da ake sayar da man fetur ɗin.
Sai dai jama’a da dama a faɗin ƙasar na fata za a samu sauƙin farashi idan matatar ta Dangote ta soma samar da man fetur a ƙasar.