An shafe lokaci ana kwan-gaba kwan-baya tsakanin kamfanin na NNPCL da kuma matatar ta Dangote dangane da batun ciniki da hada-hada ta ɗanyen mai. / Hoto: NNPCL

An soma lodin man fetur a matatar mai ta Dangote a ranar Lahadi.

Wani bidiyo da kamfanin na Dangote ya wallafa a shafin X ya nuna yadda aka soma zuba fetur cikin manyan motocin dakon mai na NNPCL.

Tun a ranar Juma’a kamfanin mai na NNPCL ya tabbatar da cewa ranar Lahadi 15 ga Satumba zai soma karɓar man fetur daga matatar ta Dangote.

Haka kuma a ranar Asabar NNPCL ɗin ya sanar da cewa akwai manyan motocin dakon mai nasa guda 100 da suka isa matatar ta Dangote tare da bayar da tabbacin cewa akwai wasu ɗaruruwa da ke kan hanya domin zuwa su yi dakon man.

Gwamnatin Nijeriyar dai ta tabbatar da cewa daga ranar 1 ga watan Oktoba, kamfanin na NNPCL zai soma bayar da ganga 385 ta ɗanyen mai a kullum ga matatar Dangote.

Sannan ita kuma matatar ta Dangote za ta bayar da fetur da man dizel wanda ya zo daidai da darajar man a kasuwa kuma a biya kuɗin a naira.

TRT Afrika