Ana sa ran karbar jirage masu saukar ungulu na Trekker nan da farkon 2026, in ji Akinboyewa. Hoto: Nigerian air force

Rundunar sojin sama ta Nijeriya tana neman samun jiragen yaƙi samfurin M-346 da Italiya ta ƙera guda 24 da kuma jirage masu saukar ungulu na AW-109 Trekker a wani bangare na shirin sabunta jiragen yaƙinta, in ji mai magana da yawun rundunar a ranar Litinin.

Mai magana da yawun rundunar sojin sama Olusola Akinboyewa ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa, tawagar karkashin jagorancin shugaban hafsan sojin saman Nijeriya Air Marshal Hasan Abubakar ta gana da shugabannin kamfanin ƙera jiragen na Italiya Leonardo S.p.A. a birnin Rome wanda ya tabbatar da cewa ana sa ran kai jirgin M-346 guda uku na farko a farkon shekarar 2025, tare da isar sauran a tsakiyar 2026.

Ana sa ran karbar jirage masu saukar ungulu na Trekker nan da farkon 2026, in ji Akinboyewa.

“Sayen M-346 da Trekker muhimman matakai ne na sabunta jiragen yaƙi,” in ji Abubakar yana mai jaddada bukatar samar da cibiyar gyaransu a Nijeriya don ba da tallafi na dogon lokaci, musamman ga jiragen yaƙin na M-346.

Ƙarin kashe kudi

Nijeriya dai ta kara yawan kudaden da ake kashewa a fannin soji a shekarun baya-bayan nan a kokarinta na daƙile hare-haren ‘yan bindiga a yankin arewa maso yammacin kasar da kuma yaƙin shekaru 15 na kungiyar Boko Haram da kungiyar Daesh da ake kira ISWAP a yankin arewa maso gabas.

A farkon wannan shekarar, kasar da ke yammacin Afirka ta karbi sabbin jiragen sama guda biyar, wadanda suka hada da jirage masu saukar ungulu na TA T129 ATAK guda biyu da aka ƙera a Turkiyya.

A watan Yuni, Nijeriya ta karbi jiragen yaki masu saukar ungulu "Huey" guda biyu, baya ga Trekkers guda biyu da ta riga ta samu, da kuma jiragen yaki 12 na Amurka A-29 Super Tucano da ta samu a shekarar 2021 domin yakar masu tada kayar baya.

Tana da jirage don isar da jirage marasa matuki na Wing Loong II na China.

TRT Afrika