Ministan Harkokin Kuɗi na Nijeriya, Wale Edun, ya ce ƙasar tana buƙatar karɓo ƙarin bashi daga ƙasashen waje domin sakawa a cikin kasafin ƙudinta duk da yake ma'aikatun ƙasar sun tara haraji fiye da yadda aka ba su umarni.
Mista Edun ya bayyana haka ne ranar Litinin a lokacin da ya je gaban 'yan majalisar dokokin tarayya na ƙasar domin yi musu bayani kan dalilan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na neman ciwo ƙarin bashi na naira tiriliyan 1.77.
“Harajin da ake samu yana da kyau, amma duk da haka ya kamata mu ƙara himma, sai dai kafin nan muna buƙatar karɓo ƙarin bashi domin bunƙasa tattalin arzikin Nijeriya," in ji Mista Edun.
Ya ƙara da cewa: “Muna buƙatar inganta ababen more rayuwa da harkokin walwala da kiwon lafiya da ilimi da bayar da tallafi ga talakawa."
Ministan na neman karɓo ƙarin bashi ne a yayin da 'yan Nijeriya suke kuka game da ƙarin matsin rayuwa da suke ciki sakamakon cire tallafin fetur da hauhawar farashin kayayyaki da suke fama da su.
Sai dai duk da haka Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya, NBS, ta fitar da wani rahoto ranar Litinin da ke cewa tattalin arzikin ƙasar ya ƙaru da kaso 3.46 a rubu’i na uku na shekarar 2024 a ma’aunin GDP.