Fadar Shugaban Nijeriya ta musanta wasu jita-jitar da ake yaɗawa kan cewa ta cim ma yarjejeniya da Faransa inda ta mallaka mata haƙƙin haƙar ma'adinanta.
Bayan ziyarar da shugaba Bola Tinubu ya kai Faransa, inda aka cim ma yarjejeniya domin haɓaka ɓangaren haƙar ma'adinai, an ta yaɗa labarai a kafafen sada zumunta kan cewa Nijeriya na shirin mallaka bangaren haƙar ma'adinanta.
Sai dai mai bai wa shugaban Nijeriya shawara kan kafafen watsa labarai Sunday Dare a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a ya yi ƙarin haske inda ya ce an cim ma yarjejeniyar ne domin ƙara haɓaka dangantaka a tsakanin ƙasashen biyu ta ɓangaren bincike da bayar da horo.
"Faransa ba za ta ƙwace iko ba. Babu wani wuri a cikin yarjejeniyar inda aka amince ko kuma aka bayar da shawara kan cewa Nijeriya za ta mallaka wa Faransa haƙƙin mallakar ma'adinai, ba kuma ta da wata illa ga tattalin arziƙin Nijeriya da tsaro kamar yadda aka rinƙa yaɗawa a shafukaan sada zumunta," kamar yadda Dare ya wallafa a shafinsa na X.
Dare ya ƙara da cewa an cim ma wannan yarjeje niyar ne da zummar haɓaka ɓangaren haƙar ma'adinai da kuma rage tasirin illolin haƙar ma'adinai a kan muhalli.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa Nijeriya na da cikakken iko kan duka albarkatun ƙasarta haka kuma yarjejeniyar da aka saka wa hannu an yi ta ne domin ƙara haɓaka ɓangaren haƙar ma'adinan ƙasar da kuma tattalin arziki.