Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ce tana bincike kan soke bizar fasinjojin ƙasar 264 da hukumomin Saudiyya suka yi bayan sun isa Jeddah daga jihohin Legas da Kano a ranar Lahadi.
An hana ‘yan Nijeriya da suka tafi a jirgin Air Peace shiga kasar Saudiyya.
A yanzu dai Ma’aikatar Harkokin Wajen Kasar na gudanar da bincike kan lamarin domin ganin ko an saɓa wa ƙa’idojin ofishin jakadanci ko na sufurin jiragen sama, in ji Alkasim Abdulkadir, mai taimaka wa Ministan Harkokin wajen kasar Yusuf Tuggar kan harkokin yada labarai a wata sanarwa a ranar Litinin.
Wannan lamari na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin Nijeriya suka kulla wasu yarjejeniyoyin kasuwanci da Saudiyya, bayan ziyartar taron Kasuwanci na Saudiyya da kasashen Afirka da aka yi a birnin Riyadh.
“Nijeriya ta halarci taron koli na Saudiyya da Afirka, inda aka tattauna kan bangarori da dama na tattalin arziki da kuma alkawura masu amfani ga juna," in ji sanarwar.
"Ma'aikatar za ta tabbatar da cewa an rage irin wadannan ayyuka da suka shafi walwalar 'yan Nijeriya a nan gaba, bisa ga dabarun 4 Ds na Shugaba Bola Ahmed Tinubu".
Jirgin ya tashi ne daga filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas ta filin jirgin Malam Aminu da ke Kano ranar Lahadi, inda ya sauka a filin jirgin sama na Sarki Abdul-Aziz da ke Jeddah a kasar Saudiyya.
Amma abin da ya bai wa ma’aikatan kamfanin jirgin Air Peace mamaki shi ne yadda hukumomin Saudiyya suka ba da sanarwar cewa an soke dukkan bizar fasinjojin.
Hakan ya faru ne duk da cewa fasinjojin sun bi duk tsarin da ya dace a lokacin da ake gudanar da rajistar bayanansu a Nijeriya bisa sa idon hukumomin Saudiyya.
Rahotanni sun ce daga baya da ofishin jakadancin Nijeriya a Saudiyya ya shiga cikin maganar, sai hukumomin Saudiyyan suka rage yawan mutanen da suka hana shigar zuwa 177 daga 264.