Layin dogo daga Kano Zuwa Maradi zai bai wa kasar Nijar damar iya shigowa da kaya ta Nijeriya:Hoto/Reuters

Nijeriya ta samu dala biliyan 1.3 don ƙarasa aikin titin jirgin ƙasa da zai haɗa Kano wato birni mafi girma a arewacin Nijeriya da Maraɗi a jamhuriyar Nijar, kamar yadda ma’aikatar harkokin sufuri ta bayyana a ranar Laraba.

Layin dogon zai ƙara bunƙasa tattalin arziki da cinikayya da zamantakewa tsakanin ƙasashen biyu.

Bashin zai fito ne daga kamfanin China Civil Engineering Construction Company (CCECC), inda zai bayar da kashi 85 cikin 100 na kuɗin, a cewar sanarwar da ma’aikatar sufurin ta fitar.

Gwamnatin Nijeriya tare da haɗin gwiwar Bankin Ci-gaban Afrika da kuma bankin Africa Export-Import Bank su ne za su ɗauki nauyin samar da ragowar kaso 15 na kuɗin.

“Samun dala biliyan 1.3 ba karamin taisiri zai yi ba wajen kammala katafaren aikin,” kamar yadda mai magana da yawun ma’aikatar sufuri Jamilu Ja’afaru ya bayyana.

A watan Yuli, wani babban kamfani na kasar Portugal Mota-Engil ya sanya hannu kan yarjejeniyar yuro miliyan 840 (dala miliyan 919) na samar da kudi da yin aikin dogon.

Ana sa ran layin dogon zai bunkasa a kasuwanci tsakanin Nijeriya da Nijar:Hoto/Reuters

Gwamnatin Nijeriya tana kokarin sake gina yankin arewacin kasar wanda yake koma baya,wani bangare na yankin ya yi ta fama da rikice-rikicen masu kaifin kishin addinin Musulunci.

Aikin layin dogon wani bangare ne na shirin gwamnati na gina layukan dogo a fadin Nijeriya don magance karancin hanyoyin sufuri wadanda hakan ke ya jawo cikas ga ci gaba a yankin a tsawon shekaru.

TRT Afrika