Nijeriya ta samar da mutum-mutumin giwa don wayar da kan jama'a kan farautar namun dawa

Nijeriya ta samar da mutum-mutumin giwa don wayar da kan jama'a kan farautar namun dawa

An samar da mutum-mutumin daga tan 2.5 na ɓaraguzan hauren giwa da mahukunta suka kama tare da lalata wa a watan Janairu.
An samar da mutum-mutumin daga nikakken hauren giwa. Hoto / Ma'aikatar Muhalli ta Nijeriya

A ranar Larabar nan ƙaramin Ministan Muhalli na Nijeriya ya ƙaddamar da wani mutum-mutumin da aka yi da hauren giwar da aka ƙwace - kuma matakin na da manufar wayar da kan kan jama'a domin daina farautar dabbobin dawa.

Mutum-Mutumin da aka mulmula ruwan toka na tattare da tan 2.5 na hauren giwayen da aka ƙwace a watan Janairu tare da ƙoƙon bayan Pangolin da darajarsu ta kai dala miliyan 11.

A yayin da yake yaye mayafin da aka lulluɓe mutum-mutumin a hedkwatar Hukumar Kula da Filayen Shaƙatawa ta Ƙasa da ke Abuja, ƙaramin Ministan Muhalli na Nijeriya Isiaq Kunle Salako ya ce ya zama "Alamar sabon fata nagari ga rayuwar namun dawa a Nijeriya".

Amma ya yi gargaɗi da cewar masu farautar namun dawan "suna da dauriya kuma ba sa daina ta'annatin cikin sauƙi".

'Ayyuka ba ƙaƙƙautawa'

"Bukatar sassan namun dawa na ci gaba da ƙaruwa a kasuwannin bayan-fage," in ji ministan. "Dole ne mu zama masu azama, mu yi aiki da dokokinmu sannan mu yi amfani da faahar zamani wajen yaƙar waɗannan ɓata-gari."

Salako ya ƙara da cewa mutum-mutumin na da kusan tsayin ɗan'adam, kuma manufar kafa shi ita ce "tunawa da ɗaruruwan giwaye da aka kashe ba bisa ƙa'ida ba da alamar himmatuwa don kare namun daji".

Tun 1989 aka haramta kasuwancin ƙasa da ƙasa na hauren giwa a ƙarƙashin Babban Taron Kasuwancin Dambobin Da Ke Fuskantar Hatsari a Matakin Ƙasa da Ƙasa.

Matattarar safara

Amma wannan mataki bai hana farauta da kasuwancin dabbobin dawa a Nijeriya ba, inda adadin dubunnan daruruwan giwayen d aake da su a kasar ya dawo kasa da 400 sabod afarautar su da ke yi, in ji Kungiyar Kare Namun Daji.

Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya Mai Yaki Da Miyagun Ƙwayoyi da Manyan Laifuka ya ce Nijeriya ta zama babbar hanyar da ake bi wajen fataucin sassan namun dawa daga Gabashi da Tsakiyar Afirka.

Daga cikin sassan dabbobin har da ƙoƙon bayan pangolin da kananan dabbobin dawa da ake amfani da su wajen haɗa magungunar gargajiya a ƙasashe irin su China da Vietnam.

TRT Afrika