Ministan tattalin arziƙi na Nijeriya, Wale Edun ya sanar da cewa gwamnatin tarayyar ƙasar ta fara aiwatar da tsarin sayar wa da matatun mai masu zaman kansu a ƙasar, ɗanyen mai bisa farashin kuɗin ƙasar, wato Naira.
Gwamnatin ta ce tun ranar 1 ga Oktoba ne aka fara aiwatar da shirin bayan da Majalisar Zartarwar Ƙasar ta yi umarni da sayar da albarkatun man, ɗanye da tataccen ta amfani da Naira.
Ranar Asabar ne daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na ma'aikatar kuɗi, Mohammed Manga ya fitar da wannan sanarwa.
Sanarwar ta ce an gudanar da taron masu ruwa da tsaki a harkar mai a ƙasar, daga ɓangaren hukumomin gwamnati da kamfanoni masu zaman-kansu. Taron ya amince da wannan muhimmin shiri da kuma fara aiwatar da shi.
Manga ya ce Nijeriya za ta ci gaba da shawo kan ƙalubalen da gwamnati ke fuskanta a harkar makamashi, da tattalin arziƙi da cigaba mai ɗorewa, da wadatar da kai.
Daidata farashin mai
Wannan mataki ya zo ne kusan makonni tara bayan da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta umarci kamfanin mai na ƙasar da ya fara sayar da ɗanyen mai ga sabuwar matatar mai ta Dangote, da kuma sauran matatun mai masu zaman kansu a cikin ƙasar.
Tsarin yana da manufar daidaita farashin mai da ake sayarwa a gidajen mai, kuma ana fatan tsarin ya kawo rangwame da tsayuwar farashin nau'o'in mai da al'ummar ƙasar ke saya.
Sayar da man da Naira, maimakon dalar Amurka zai rage matsin da ke haifar da tsadar dala a ƙasar, da yawan kuɗaɗen waje da ƙasar ke tattali, wanda zai taimaka wajen daidata farashin musayar Naira da dala, da shawo kan hauhawar farashin kayayyaki.
Bugu da ƙari tsarin zai taimaka wa matatun mai masu zaman kansu cikin ƙasar, wajen rage dogaro kan safarar ɗanyen mai daga ƙasashen waje, wanda zai sa su adana dalar da suke samu, baya ga taimakawa wajen wadatuwar mai a cikin ƙasar.