Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bukaci Majalisar Dinkin Duniya da ta zama mai daukar matakai da wuri don magance matsalolin talauci, tsaro da sace albarkatun kasa na Afirka da ke damun kasashen nahiyar, in ji kakakinsa.
Tinubu ya yi wannan kira ne a lokacin da ya gana da Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres a ranar Laraba, a wani bangare na ganawar bayan fage a yayin Babban Taron Majalisar a New York, in ji wata sanarwa da kakakinsa Ajuri Ngelale ya fitar a ranar Alhamis din nan.
Shugaban na Nijeriya ya kuma ce bata-gari da ke aikata munanan ayyuka da suka hada da fasa kaurin albarkatun kasa da makamai, na tatsar dukiyar Afirka, suna kuma hana ta zama lafiya.
Sanarwar ta rawaito Tinubu na cewa "Muna fama da kalubalen barayi da ke kutsawa kasashenmu suna zaluntar mutanenmu ta hanyar sanya su hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba, suna sace zinare da arzikinmu suna zuwa suna kai wa kasashen da suka ci gaba,"
Ya ce "A yanzu za mu fusata, za mu tuhumi duk wani motsi da manufa. Za mu dakatar da abun da ke faruwa," inda ya kuma yi kira ga "samar da ƙwaƙƙwaran hadin kai" daga Majalisar Dinkin Duniya.
Babban garambawul
Tinubu ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta sauya daga teburin tattauna wa na kasa da kasa, zuwa cibiyar daukar matakai da wuri, inda ya yi nuni ga muhimmancin magance matsalolin talauci da tsaro.
Sanarwar ta kuma ce a nasa jawabin, Guterres ya bayyana bukatar babban garambawul a MDD don magance raunin hukumomi da inganta karfin daukar matakai da yanke hukunci daga kasashe masu taso wa.
An rawaito Guterres na cewa "A yanzu mun fahimci bukatar yin sauye-sauye a hukumomi don wakiltar kowanne bangare na duniya kamar yadda take a yau."
A jawabin da ya yi a Zauren Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata, Tinubu da ke shugabantar ECOWAS ya soki juyin mulkin da ake samu a Yammacin Afirka, ya kuma yi alkawarin taimaka wa don dawo da aiki da kundin tsarin mulki a Nijar.