Ɗan awaren Biafra Simon Ekpa na fuskantar tuhume-tuhumen da suke da alaƙa da ta'addanci. / Hoto: Simon Ekpa/ X

Nijeriya ta yi maraba da kama jagoran 'yan awaren Biafra a Finland inda ake zarginsa da ayyukan ta'addanci da kuma tunzura jama'a domin tayar da hankali.

Simon Ekpa, wanda yake iƙirarin jagorantar "Biafra Republic Government in Exile", yana tsare a kurkuku bayan da wata kotun Finland ta bayar da umarnin tsare shi a ranar Alhamis.

Yana fuskantar tuhume-tuhume waɗanda ke da alaƙa da kiraye-kirayen da ake yi a shafukan sada zumunta na ɓallewar Biafra a kudu maso gabashin Nijeriya.

Nijeriya na cikin "farin ciki" bayan kama Ekpa da hukumomin Finland suka yi, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar tsaron ƙasar Janar Tukur Gusau ya shaida wa TRT Afrika.

"Muna fatan za su tasa ƙeyarsa zuwa Nijeriya nan take, ta yadda zai gurfana a gaban kotu, ya amsa laifukan da ake zarginsa da aikatawa na ta'addanci da harzuƙa al'umma su tayar da rikici musamman a kudu maso gabashin Nijeriya," in ji Janar Gusau.

Hukumomin Najeriya "suna ta kira ga duk wadanda abin ya shafa da su tabbatar an tasa ƙeyar ɗan ta’addan, Simon Ekpa zuwa Nijeriya, domin ya fuskanci shari’a," in ji shi.

Ekpa, wanda ke riƙe asalin ɗan Nijeriya ne kuma mai takardar zama a Finland, wakili ne na wata jam'iyya ta National Coalition Party a birnin Lahti da ke arewacin Helsinki a ƙasar ta Finland inda yake aiki a matsayin mamba a kwamitin sufuri.

An san shi a matsayin jagoran ɗayan ɓarin ƙungiyar IPOB mai fafutikarkafa ƙasar Biafra.

Bayan kama shi, hukumomi a Finland sun gurfanar da ɗan awaren mai shekara 41 a gaban kotun gundumar Paijat-Hame a ranar Alhamis.

An kama Ekpa tare da wasu mambobin kungiyar su hudu a farkon makon nan, in ji ‘yan sandan Finland.

Masu binciken na kasar Finland sun kuma bukaci da a tsare sauran mutane hudu a gidan yari bisa zargin su da daukar nauyin ayyukan Ekpa.

"Mun gode gode Finland. Muna jiranka nan ba da jimawa ba Firaminista," kamar yadda Dada Olusegun ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, a cikin wani martani da ya mayar ga Ekpa wanda ya bai wa kansa Firaminista.

A shekarun baya-bayan nan dai mahukuntan Nijeriya na kokarin ganin sun dakile wani yunkuri na masu neman ɓallewa daga yankin kudu maso gabashin kasar karkashin jagorancin kungiyar IPOB, inda gwamnatin kasar ke zargin kungiyar da kai munanan hare-hare kan fararen hula da jami'an tsaro a yankin.

Jagoran ƙungiyar Nnamdi Kanu ya jima yana fuskantar shari'ar kan zargin ta'addanci.

Irin wannan ta'addancin na IPOB ne ya jawo yaƙin basasa a Nijeriya a shekarun 1960 inda fiye da mutum miliyan guda suka rasu.

TRT Afrika