Hukumar Kula da Sa Ido a kan Abinci da Magunguna ta NIjeriya NAFDAC, ta amince da rigakafin cutar maleriya na R21 da Cibiyar Serum ta Indiya ta samar.
Wannan mataki ya sa kasar ta zama ta biyu da ta amince da rigakafin wanda Jami’ar Oxford ta Birtaniya ta kirkira, a duniya baya ga Ghana wacce ta sanar da amincewa da shi a makon da ya gabata.
Shugabar hukumar NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bayyana hakan a ranar Litinin a wajen wani taron manema labarai a Abuja, Farfesa Adeleye ta kara da cewa an samar da rigakafin ne don kare yara ‘yan wata biyar zuwa 36 daga kamuwa da cutar maleriya.
Ta ce kasar na sa ran samun rigakafi a kalla ta mutum 100,000 a matsayin tallafi kafin a fara samunsa a kasuwa inda Hukumar Kula da Lafiya a matakin farko za ta kula da hakan.
A cewar Farfesa Mojisola rigakafin maleriya na R21 ya cika sharuddan kasa da kasa da suka dace.
Ta kara da cewa Kwamitin hadin gwiwa da ke duba kan maganin ya amince cewa bayanan da aka tattara na maleriya R21 sun cike duka sharudda da matakan sahihanci da inganci.