Nijar da damke masu safarar miyagun kwayoyi tsakanin Nijeriya da kasar don kaiwa kasashen Arewacin Afirka

Hukumar ‘yan sandar kasar Nijar ta yi nasarar kama gungun masu safarar kwayoyi tsakanin kasa da kasa.

Wani bangaren ‘yan sandar kasar mai yaki da safarar miyagun kwayoyi, wato L’Office Central de Répression du Trafic Illicite des Stupéfiants (OCRTIS) ne, ya yi wannan kamun.

Gungu na farko ya kunshi mutum tara ‘yan asalin Nijar da suke safarar magani mai sa maye na Tramadol, da kuma wata kwaya nau’in Pregabalin.

Yawancin kwayoyin ana safarar su ne daga makwabciyar kasar, Nijeriya, inda sukan biyo ta yankin Maradi da ke kan iyaka.

Daga Maradi a kan tura kwayoyin ne zuwa garin Agadas, sannan a shige da su kasar Libiya ko wasu kasashe na arewacin Afirka.

Gungun mutanen da kamen ya ritsa da su, suna kokarin kai kwayoyin ne zuwa Libiya, inda aka damke su a iyakar garin Maradi da Agadas.

Shi kuwa gungu na biyu, ya kunshi mutum daya ne dan asalin Nijeriya, wanda aka kama shi a garin Arlit kafin ya ketara Libiya, da nufin safarar kwayoyin zuwa kasar Aljeriya.

Jami’an tsaro ne suka dakatar da shi a wani shingen bincike na garin Arlit, yayin da yake dauke da fakitin kwayoyin, wadanda ya hadiye don gudun kar a gane.

Yayin gabatar da masu laifin a birnin Yamai, babban mai shigar da kara na gwamnati, Malam Chaibou Moussa ya yaba wa jami'an tsaron game da wannan kamu.

TRT Afrika