Nijar ta ɗauki matakin ne kwanaki kaɗan bayan maƙociyarta Mali ta yanke hulɗar diflomasiyya da Ukraine./Hoto:Fadar Gwamnatin Nijar

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun sanar da yanke hulɗar jakadanci da Ukraine "nan-take", bayan sun zargi ƙasar da goyon bayan "ƙungiyoyin 'yan ta'adda"

Kakakin gwamnatin mulkin sojin Jamhuriyar Nijar Amadou Abdramane ne ya bayyana ɗaukar matakin ranar Talata da maraice a wata sanarwa da ya karanto ta gidan talbijin na ƙasar.

Ya ƙara da cewa za su shaida wa Majalisar Ɗinkin Duniya wannan lamari domin ta tattauna kan "kutsen" da Ukraine take yi a yankinsu.

Nijar ta yanke hulɗar jakadanci da Ukraine ne kwana biyu bayan maƙociyarta Mali ta sanar da ɗaukar irin wannan mataki, sakamakon zargin da ta yi wa mahukuntan birnin Kiev na hannu a hare-haren da 'yan ta'adda suka kai wa sojojinta inda suka kashe da dama daga cikinsu a kwanakin baya.

Daga cikin waɗanda aka kashe a harin da 'yan ta'adda suka kai wa sojojin a yankin Tinzaouaten da ke arewacin Mali har da sojojin haya na Wagner na Rasha waɗanda ke taimaka wa sojojin ƙasar.

"Gwamnatin Jamhuriyar Nijar tana goyon bayan gwamnati da al'ummar Mali, don haka ta yanke shawarar katse hulɗar diflomasiyya da Ukraine nan-take," a cewar Abdramane.

Ranar Lahadin da ta gabata, mai magana da yawun gwamnatin Mali Kanar Abdoulaye Maiga ya fitar da sanarwa da ke cewa "Gwamnatin riƙon ƙwarya ta Jamhuriyar Mali ta yi matuƙar kaɗuwa da bayanan da kakakin hukumar leƙen asiri ta sojin Ukraine Mr. Andriy Yusov, ya yi cewa Ukraine na da hannu a mummunan hari na rashin imani da gadara da 'yan ta'adda matsorata suka kai wanda ya yi sanadin mutuwar jami'an tsaron Mali a yankin Tinzaouaten, tare da lalata kayayyaki".

Daga nan ya bayyana cewa sun yanke hulɗar jakadanci da ƙasar.

Mali da Nijar da kuma Burkina Faso, waɗanda sojoji suke mulki, sun sha alwashin kasancewar 'yan'uwan juna tare da ƙulla ƙawance bayan ƙungiyar ECOWAS ta dakatar da Nijar daga cikinta sakamakon juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023.

TRT Afrika