Daga cikin wadanda aka kama har da 'yan kasashen Aljeriya da Chadi da Somaliya.

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun kama akalla mutane 245 da ake zargi da alaka da kungiyoyin ‘yan ta’adda a ci gaba da gudanar da ayyukan yaki da miyagun laifuka da tada kayar baya, kamar yadda jami’ai suka bayyana a jiya Alhamis.

Hukumar da ke yaki da ta’addanci da kuma manyan laifuffukan kasa da kasa ta Jamhuriyar Nijar ce ta yi kamen, kamar yadda cibiyar Integrated Operation Coordination Center (CICO) ta bayyana.

Da yawa daga cikin wadanda ake tsare da su ana zargin 'yan kungiyoyin masu dauke da makamai ne da ke da hannu wajen yin garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka, wadanda ke gudanar da ayyukansu a kan iyakar Nijar da Nijeriya, inda 'yan kungiyar Boko Haram ke da karfi.

An kara kama wasu a kusa da kan iyakar Mali da Nijar, yankin da kungiyar Support Group for Islam and Muslim (JNIM) ke gudanar da ayyukanta, da kuma yankin Agadez da aka fi sani da hakar zinare.

Daga cikin wadanda aka kama har da 'yan kasashen Aljeriya da Chadi da Somaliya.

Jami’an tsaro sun kuma ƙwace sama da kilogiram 559 na ƙwayoyi da suka haɗa da nauyin ƙwayoyi har 108,381, tare da kama masu safarar mutane 139.

CICO ta bayyana cewa wadannan ayyuka wani bangare ne na kokarin da ake na wargaza hanyoyin sadarwa a yankin.

Kamen dai ya zo ne a daidai lokacin da rundunar sojin kasar ta kaddamar da wasu manyan hare-hare guda biyu da suka hada da Operation Almah a yankin Tillaberi da ke gefen hagu na Kogin Neja da kuma Operation Garkoua da ke yankin Agadez da nufin kawar da masu aikata laifuka.

Nijar tare da Burkina Faso da Mali makwabciyarta, sun fice daga kungiyar ECOWAS a watan Satumban da ya gabata, bayan da kungiyar ECOWAS ta yi barazanar shiga tsakani na soji bayan juyin mulkin Nijar a watan Yuli.

Tun da fari dai, kasashen uku sun kafa kawancen kasashen yankin Sahel tare da sanar da kafa rundunar soji ta hadin gwiwa domin tunkarar kalubalen tsaro da kungiyoyin 'yan ta'adda ke yi a yankin.

AA