Kungiyar mai mambobi 88 "Faransa na amfani da ita a matsayin makami don kare muradun Faransa in ji sojin Nijar. / Photo: AFP Archive

Kasar Nijar ta dakatar da duk wata hadin gwiwa da kungiyar kasashe masu amfani da harshen Faransanci (OIF), kamar yadda shugabannin sojojinta suka bayyana, yayin da ta ci gaba da yanke alaka da kasar da ta yi mata mulkin mallaka na Faransa.

Kungiyar mai mambobi 88 "Faransa na amfani da ita a matsayin makami don kare muradun Faransa", in ji mai magana da yawun gwamnatin mulkin Nijar a jawabin da ya yi a gidan talabijin na kasar da yammacin jiya Lahadi.

A watan Yuli ne sojoji suka ƙwace juyin mulki a Nijar, lamarin da Faransa da sauran ƙawayenta na Yammacin Duniya suka yi Allah wadai da shi.

Nan da nan kuma gwamnatin mulkin sojin ta kori dakarun Faransa daga ƙasar, waɗanda suke taimakon ƙasar wajen yaƙi da masu tsattsauran ra'ayin da suka shafe kusan shekara 10 suna ta da rikici a ƙasar.

Tuni Ƙungiyar OIF ma ta dakatar da mafi yawan ayyukan hadin gwiwarta da Nijar a makon da ya wuce saboda juyin mulkin, amma ta ce za ta ci gaba da aiwatar da waɗannan shirye-shiryen "da kai tsaye suke shafar al'umma, da kuma masu ƙoƙarin ganin an dawo da dimokuraɗiyya."

Manufar kungiyar ita ce inganta harshen Faransanci da tallafawa zaman lafiya da dimokuradiyya, da ƙarfafa ilimi da ci gaba a kasashen da ke amfani da harshen Faransanci a duniya, waɗanda yawancinsu tsoffin ƙasashen Faransa ne.

Reuters