Ko a bara sai da Nijar ɗin ta ƙaddamar da wata babbar tashar sola wadda ke da fafafayen na sola fiye da 55,000 inda tashar ke da ƙarfin samar da megawatts 30 na lantarki. / Hoto: RTN

Kamfanin Samar Da Wutar Lantarki na Nijar NIGELEC ya ƙara adadin wutar lantarkin da yake samarwa da megawatts 18 a ƙasar.

Hakan ya biyo bayan ƙaddamar da injinan samar da lantarki masu amfani da man dizal masu ƙarfin megawatts 22.5 da ƙasar Maroko ta bai wa Nijar kyauta.

An kammala aikin samar da lantarkin ne a cikin watanni huɗu maimakon watanni 18 waɗanda a baya aka ɗaukar wa aikin.

Samun ƙarin lantarkin a yanzu zai bai wa kamfanin lantarki na Nijar damar ƙara rarraba wutar yadda ya kamata musamman a Yamai babban birnin ƙasar da kuma makwabtan jihohi.

Sabuwar tashar lantarkin wadda ke a Yamai 2, na ɗauke da manyan janaretoci tara waɗanda kowane ke da ƙarfin megawatts 2.5.

Ma’aikatan lantarkin Nijar da na Maroko ne suka yi haɗin gwiwa domin aikin haɗa janaretocin ba dare ba rana domin tabbatar da cewa Nijar ɗin ta samu isashiyar wutar lantarki.

Ƙasar ta Nijar ta ƙara mayar da hankali wurin haɓaka lantarkin ƙasar tun bayan da Nijeriya ta katse wa Nijar ɗin lantarki a kwanakin baya a ɗaya daga cikin takunkuman da ƙungiyar ECOWAS ta saka wa ƙasar bayan sojoji sun yi juyin mulki.

Ko a bara sai da Nijar ɗin ta ƙaddamar da wata babbar tashar sola wadda ke da fayafayen na sola fiye da 55,000 inda tashar ke da ƙarfin samar da megawatts 30 na lantarki.

TRT Afrika