Kasashen uku duka suna karkashin mulkin sojoji. / Hoto: Others

Ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso a ranar Lahadi sun fitar da sanarwar haɗin gwiwa inda suka bayyana cewa sun fice daga ƙungiyar ECOWAS nan-take.

Shugabannin kasashen yankin Sahel uku sun fitar da wata sanarwa inda suka ce "mataki ne" suka dauka na ficewa daga kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka "ba tare da bata lokaci ba".

“Bayan shekaru 49, jajirtattun al'ummar Burkina Faso da Mali da Nijar cikin nadama tare da nuna rashin jin dadinsu na ganin cewa kungiyar (ECOWAS) ta kauce daga akidar kakanninmu da suka kafata ta kishin Afirka,” kamar yadda Kanal Amadou Abdramane, mai magana da yawun sojojin Nijar, ya bayyana.

"Kungiyar ta gaza wurin taimaka wa waɗannan ƙasashe a yaƙin da suke yi da ta’addanci da rashin tsaro,” kamar yadda Abdramane ya kara da cewa.

Kasashen wadanda ke fama da matsalar masu ikirarin jihadi da talauci, sun ta samun matsaloli da ECOWAS tun bayan da aka yi juyin mulki a Nijar a Yulin bara da kuma na Burkina Faso a 2022 da na Mali a 2020.

Duka ƙasashen uku a kwanakin baya ECOWAS ta dakatar da su inda ta saka musu takunkumai masu tsauri.

A watan Satumbar bara ne ƙasashen suka ƙulla ƙawancen Sahel Alliance ko kuma Liptako-Gourma.

Ƙasashen sun ce wannan yarjejeniyar da suka yi za ta mayar da hankali wurin ci gabansu ta fannin tsaro da tattalin arziki.

Janyewar sojojin Faransa daga yankin na Sahel ya ƙara saka fargaba kan sha’anin tsaro a yankin na Sahel, inda ake fargabar cewa yaƙin zai iya ƙara bazuwa zuwa Ghana da Togo da Benin da Ivory Coast.

Firaiministan da sojojin Nijar suka naɗa a ranar Alhamis ya caccaki ECOWAS inda ya ce ba su da kyakkyawan nufi bayan ƙungiyar ta ƙi zuwa wani taro wanda aka shirya yi a Yamai.

TRT Afrika