Netanyahu

1700 GMT –– Yana da kyau a yi amfani da shirin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza da Amurka ta samar ta hanya mai kyau — Ministocin Wajen Kasashen Larabawa

Ministocin Harkokin Wajen kasashen Saudiyya da Jordan da Hadaddiyar Daular Larabawa da Qatar da Masar sun bayyana cewa yana da matukar muhimmanci a yi aiki da gaske da gaskiya kan shawarar da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar da za ta kai ga tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Saudiyya rawaito.

Ministocin Harkokin Wajen sun gana ta intanet don tattaunawa kan shawarar Biden da ma batun kokarin Qatar da Masar don sasanta Isra'ila da Falasdinu kan batun mutanen da ake garkuwa da su, wadda ake sa rai za ta kai ga tsagaita wuta da kai isasshen agaji zuwa Gaza, in ji SPA.

1410 GMT –– Netanyahu ya ce Biden ya ɗauki ɓangare a shirin yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza — Tel Aviv

Wani mai magana da yawun gwamnatin Isra'ila ya ce Firaiminista Benjamin Netanyahu ya kalli shirin tsagaita wuta da yarjejeniyar yin garkuwa da mutane a Gaza da shugaban Amurka Joe Biden ya gabatar a matsayin "wadda ya ɗauki ɓangare".

Kakakin gwamnatin kasar David Mencer ya ambato Netanyahu yana cewa, "Bayanan da Shugaba Biden ya gabatar sun nuna bangaranci," yana mai cewa "za a dakatar da yakin da nufin mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su" daga bisani kuma za a tattauna kan "yadda za a cimma burin yakin na kawar da Hamas".

Isra'ila na ci gaba da kai hare-hare Gaza inda zuwa yanzu mutum 36,479 suka mutu tun ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

1238 GMT Hare-haren Isra'ila sun sake kashe mutum 11 a Gaza

Jami'an kiwon lafiya na Falasdinawa sun ce harin da Isra'ila ta kai cikin dare ya kashe mutum 11 cikin daren Litinin, ciki har da mace daya da kananan yara uku a tsakiyar Gaza.

Wani harin da aka kai kan wani gida a sansanin 'yan gudun hijira da aka gina a Bureij da yammacin ranar Lahadi ya kashe mutum hudu ciki har da yara uku.

Hari na biyu a ranar Litinin ya kashe mutum bakwai ciki har da mace daya a sansanin ‘yan gudun hijira na Nuseirat. Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce adadin wadanda suka mutu a yakin yanzu ya kai 36,479.

1125 GMT — An tilasta wa sama da mutum miliyan ɗaya gudun hijira daga Rafah — UNRWA

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce yaƙin da Isra'ila ke yi a kudancin Gaza ya tilasta wa sama da mutum miliyan guda barin gudun hijira daga Rafah.

Rundunar Sojin Isra'ila ta buƙaci farar hula su matsa can gaba da Rafah, kimanin kilomita 20.

Falasɗinawa da dama sun koka kan cewa hare-haren Isra'ila na kashe su a duk inda suka je, inda suke da gararamba ta ko ina a Gaza a 'yan watannin da suka gabata.

UNRWA ta ce dubban iyalai yanzu haka suna neman mafaka a wuraren da suka lalace da kuma ruguje a cikin birnin Khan Younis, inda hukumar ke samar da muhimman ababen buƙatu na yau da kullum a gare su.

0146 GMT — Blinken ya kira jami'an Isra'ila don tattaunawa a kan batun yarjeniyar tsagaita wuta ta Gaza

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken ya kira wasu manyan jami'an Isra'ila domin tattaunawa kan shirin tsagaita wuta a Gaza, in ji Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka.

Blinken ya yi magana da Ministan tawagar yaƙin Benny Gantz da kuma Ministan Tsaro Yoav Gallant, kamar yadda bayanai suka nuna.

A duka kiraye-kirayen biyu, ya yaba wa Isra’ila kan wannan shawara, wadda shugaban Amurka Joe Biden ya zayyana, ya kuma ce wajibi ne Hamas ta amince.

TRT Afrika da abokan hulda