NDLEA ta kama ƙasurgumar mai fataucin ƙwaya da ɗan  Nollywood kan zargin fataucin miyagun ƙwayoyi

NDLEA ta kama ƙasurgumar mai fataucin ƙwaya da ɗan  Nollywood kan zargin fataucin miyagun ƙwayoyi

Sanarwar hukumar ta NDLEA ta ce ta kama mata biyu masu haɗa kek da ƙwayoyi ga ɗalibai.
Janar Bubu Marwa ne shugabn hukumar NDLEA:Hoto/NDLEA

Jami’an hukumar yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya (NDLEA) sun kama wata shahararriyar mata a Legas, Alhaja Aishat Feyisara Ajoke Elediye, da kuma wani mai shirya fim na Nollywood, Emeka Emmanuel Mbadiwe kan zargin fataucin miyagun ƙwayoyi.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Femi Baba Femi, ya fitar ta ce Alhaja Aishat wadda ake yi wa laƙabi da “Iya Ruka” a tsakanin masu fataucin ƙwaya ta daɗe cikin waɗanda hukumar take nema, sai dai ba a gane haƙiƙanin wace ce ita ba har sai da aka kama ta ranar 1 ga watan Janairun 2025.

“A zahiri dai, Alhaja Ajoke ‘yar kasuwa ce wadda ke shigowa da tufafi da takalma daga China, amma a asirce tana fataucin ƙwaya sosai,” in ji sanarwar NDLEA wadda ta ce matar na cikin matan da aka fi jin sunayensu a Legas.

“Asirinta ya tonu ne ranar Laraba 1 ga watan Janairun shekarar 2025 lokacin da jami’an hukumar NDLEA bisa bayanan sirri suka kama wata babbar mota fara ƙirar Isuzu ɗauke da buhuna 44 na wiwi da suka kai kilo 1,540, wadda wani mai shekara 41 mai suna Abideen Adio yake ja,” in ji Babafemi.

Bayan haka ne jami’an hukumar suka kama ta a gidanta da ke unguwar Okota a Legas.

Kazalika hukumar ta kama wani mai shirya fim na Nollywood, Emeka Emmanuel Mbadiwe, a wani otel a Lekki bayan an kama abokin aikinsa , Uzoekwe Ugochukwu James a rukunin gidajen Ajao da ke Ikeja.

Sanarwar NDLEA ta ce an kama Ugochukwu ne a lokacin da ya je karɓar ƙullin tabar wiwi mai ƙarfi da ake ce wa LOUD wadda nauyinta ya kai kilo 17.30 wadda ta iso tashar jirgin Murtala Mohammed ranar 24 ga watan Disambar shekarar 2024.

A jihar Kwara kuwa hukumar ta kama Khadijat Abdulraheem, mai shekara 24, da kuma Ayomide Morakinyo mai shekara 20 ranar 29 ga watan Disambar shekarar 2024 a hanyar Jami’ar Ilorin kan bayanan sirrin cewa suna haɗa kek da miyagun ƙwayoyi.

“Bayan an binciki gidansu an samu kek 42 da aka haɗa tare da su,” in ji sanarwar NDLEA.

TRT Afrika