Hukumar Kididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar da jerin nau’ukan kayan abinci da farashinsu ya tashi daga shekarar 2022 zuwa wata hudun farko na 2023.
A wani rahoto na zababbun kayan abinci na 2023 da ta fitar, hukumar ta ce an rinka sayar da kilogiram daya na nama a kan naira 2,479.61 a watan Maris na 2023.
Wannan rahoto ya sake fayyace hauhawar farashin kayayyaki da aka jima ana fama da ita a kasar.
“Hakan na nuna cewa an samu kari da kashi 25.05 cikin 100 a kan yadda aka sayar da duk kilogiram daya a kan farashin naira 1,982.92 na watan Maris din 2022 da kuma hauhawar kashi 1.38 cikin 100 da ake samu wata-wata daga naira 2,445.96 a watan Fabrairun 2023,” in ji rahoton.
Kazalika farashin kilo daya na tumatur ya karu da kashi 13.81 cikin 100 a kan farashin watan Maris na 2022 daga naira 409.96 zuwa naira 466 a Maris din 2023.
Yayin da aka samu raguwar farashin nasa na wata-wata zuwa kashi 0.32 a watan Maris na 2023.
NBS ta kuma ce farashin kilo daya na jan wake ya tashi da kashi 13.13 cikin 100 inda aka sayar da shi kan N596.96 a Maris din 2023 idan aka kwatanta da na watan Maris din bara da aka sayar a kan N527.66.
Sai kuma kilo daya na albasa da farashinsa ya karu da kashi 17.37 idan aka kwatanta da yadda aka sayar da shi a bara warhaka.
A Maris din 2022 an sayar da kilo daya na albasar a kan N378.59 yayin da a Maris din 2023 ya kama N444.37, amma farashin ya sauka da kashi 1.27 a wata-wata daga Fabrairun 2023.
Ita kuwa doya farashin kilo daya ya karu da 25.30% idan aka kwatanta da na bara warhaka, wato N353.56 a Maris na 2022 zuwa N443.02 a Maris din 2023.
An sayar da kwalbar man girki daya a kan N1,220.62 a watan Maris din 2023 abin da ke nuna cewa an samu hauhawa da 25.80% daga farashin N970 da aka sayar da shi a Maris din 2022.
Ga dai jerin wasu kayayyakin da jihohin da suka fi tsada ko araha
- Farar masara ta fi tsada a Jihar Akwa Ibom (N512.50) yayin da ta fi araha a Jihar Kano (N237.31)
- Jar masara ta fi tsada a Akwa Ibom (N577.16) yayin da ta fi araha a Jihar Kaduna (N221.83)
- Kwai kiret daya ya fi tsada a Enugu (N1161.16) ya kuma fi araha a Jihar Kogi N580.33)
- Danyen kifi tarwada ya fi tsada a Jihar Edo N2250.00 yayin da ya fi araha a Jihar Bauchi (N798.32)
- Jan wake ya fi tsada a Jihar Ebonyi (N906.00) ya fi araha a Jihar Kebbi (N352.70)
- Biredi mai yanka-yanka ya fi tsada a Jihar Abia (N770.32) yayin da ya fi araha Filato (N350.00)
- Shinkafa ‘yar gida ta fi tsada a Jihar Rivers (N738.28) ta kuma fi araha a Jihar Jigawa (N368.39)
- Man girki ya fi tsada a Jihar Abia (N1618.21) ya kuma fi araha a Jihar Binuwai
- Nama mai kashi ya fi tsada a Jihar Anambra (N3107.44) ya fi araha a Jihar Kogi (N1778.00)
- Manja ya fi tsada a Jihar Kaduna (N1345.24) ya fi araha a Jihar Kwara (N700.24).
Me wannan hauhawa ke nufi?
Hauhawar farashin kayan abinci abu ne da dama tuni masana sun hango faruwar sa har ma sun yi ta maganganu tun da jimawa.
Wani mai sharhi kan tattalin arziki kuma shugaban kamfanin Castke Ridge da ke Abuja, Muhammad Auwal Mahmud, ya ce hauhawar farashin nan ta samo asali kan wasu abubuwa da ke faruwa a kasa.
“Misali kamar a Nijeriya mun samu matsaloli daban-daban irin na tsaro musamman na masu garkuwa da mutane, wadda ta jawo matsalar da mafi yawancin manoma na jin tsoron zuwa gonakinsu, lamarin da ya jawo raguwar samar da kayan abinci.”
Masanin ya ce abu na biyu da ya jawo hakan shi ne abin da ake kira da “Visual circle of poverty,” wato rashin samun abin da mutane za su ci su kuma sayar daga abin da suke nomawa, ta yadda za a samu gibi sosai.
“Wato ma’ana shi manomi bai samu ya noma ba balle ya kai kasuwa ya sayar, shi ma dan kasuwa bai samu ya saya daga wajen manomi don ya sayar ga masu bukata ba balle har ya samu riba.
“Sannan ga masu bukatar saye kuma da yawa amma kayan ba su wadata ba, to daga nan sai farashi ya fara hauhauwa. Hakan sai ya jawo hawan farashin da kuma rashin kudi a wajen mutane,” ya ce.
Abu na uku da masanin ya ce ya ta’azzara lamarin shi ne shigar da kayayyakin abinci daga kasashen waje.
“Yakin Rasha da Ukraine ya ta’azara lamarin shigar da abinci daga kasashen waje inda ba a samun wasu muhimman abubuwa da ake shigowa da su da babu a nan.
Hakan na sa farashi ya ta’azzara saboda an samu karancin abun. Wannan shi ne halin da muke ciki,” in ji shi.
Malam Auwal ya jaddada cewa wadannan duka abubuwa ne tabbatattu da masana suka yi ta bayyana cewa za su faru kuma an yi ta nuna wa gwamnati.
Sai dai ya yaba wa gwamnatin Nijeriya karkashin Shugaba Muhammadu Buhari kan kokarin da ya ce ta yi wajen fito da tsare-tsaren bunkasa samar da abinci inda ta yi kokarin neman mutane da ba su kudade ta hanyar shirye-shiryen da ta bullo da su.
“Amma har yanzu hakan bai yi tasirin da ya kamta ya yi ba saboda dalilai da yawa da suke a bayyane kowa na gani,” in ji mai sharhin.
Mataki na gaba da ya kamata gwamnati ta dauka
A ganin masanin, mataki na gaba da ya kamata hukumomi su dauka shi ne mayar da hankali wajen yadda za a wadata kasa da abinci.
“Muna da fili na noma kuma muna da kasa mai albarka da duk abin da muka noma zai fito ya yi albarka.
“Tun da muna da wannan da kuma shirye-shiryen gwamnati da yawa, to kamata ya yi hukuma ta koma ta duba irin nasarorin da aka samu cikin abubuwan da aka yi da kuma matsalolin da aka fuskanta.
“Ta nan ne za a iya ganewa tare da tantnace shin wadanne matsaloli ne aka samu don gyaransu gaba, sannan a mayar da hankali sosai wajen samar da abincin nan don yana da matukar muhimmnaci,” ya jaddada.
Malam Auwal ya kuma ba da misali da wani shiri na ci gaba da aka yi a kasar a zamanin mulkin Janar ibrahim Babangida mai taken “Perspective and Rolling Plan,” da ake dibar shekaru misali 20 ko 30, da za a dinga zama duk shekara ana duba wadanne matsaloli aka samu, yaya za a gyara kuma yaya za a bunkasa?
"To idan aka dauki irin wannan salon shi ne za a samu nasara. Amma idan aka ci gaba da tafiya a kan turbar da ake a yanzu to za a yi ta samun matsaloli.
“Lallai dole a dinga yin abubuwan da ke bukatar gyara sosai a kansu da ya kamata gwamnati ta mayar da hankali don yin hakan. Sannan a duba harkar noma da gaske ba da wasa ba.