Hukumar da ke kula da ingancin abinci da maguna ta Nijeriya NAFDAC ta rufe shaguna fiye da 3,000 da ke sayar da jabun magunguna a kasuwar sayar da magunguna ta Idumota da ke Legas.
Hukumar ce ta tabbatar da hakan a shafinta na X inda ta wallafa hotunan wasu daga cikin jabun magungunan da ta kama a lokacin samamen.
A lokacin da ta kai samamen, hukumar ta gano wasu abubuwa masu ɗaga hankali waɗanda suka haɗa da alluran rigakafin da aka ajiye a wurare maras kyau, da ɗakuna da babu wurin shigar iska, wanda hakan zai iya barazana ga lafiyar jama’a.
Hukumar ta NAFDAC ta gano wasu ɗumbin magungunan da aka haramta amfani da su masu matuƙar haɗari, daga ciki har da allurar Analgin, da kuma magungunan cutar HIV da aka karkatar.
Haka kuma hukumar ta bayyana cewa ta gano magunguna masu yawa waɗanda suka lalace inda ake shirya sauya musu mazubi domin kai su kasuwa.
A ‘yan kwanakin nan hukumar NAFDAC na yawan gano wuraren da ake ɓoye lalatattun magunguna da kayan abinci.
Ko a ‘yan kwanakin nan sai da hukumar ta buƙaci hukumomin ƙasar kan a fara yanke hukuncin kisa ga waɗanda ke safarar jabun magunguna.