NAFDAC

Hukumar da ke Kula da Inganci Abinci da Magunguna ta Nijeriya, NAFDAC ta gurfanar da wasu mutum uku da kuma wani kamfani a gaban Babbar Kotun Jihar Kano bisa zargin su da samar da kuma sayar da magunguna na jabu da marasa inganci.

Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta ce ana tuhumar mutanen Mr. Amao Gideon da Alumona Godwin Okwiludili da kuma Hillary Onah Paul Chigozie, da laifuka biyar, “bayan kama su da laifin samar da magunguna marasa kyau da babu ingantattun sinadarai a cikinsu.”

NAFDAC ta ce magungunan sun haɗa da:

  • Garin maganin Asian Ampicillin na yara (125mg + Cloxacillin 125mg/5ml children.)
  • Garin maganin Erythromycin na yara (125mg/5ml).
  • Maganin maleriya na yara Artil-Go (Artemether 20mg + Lumefantrine 120mg/5ml)

Hukumar ta ƙara da cewa gwaje-gwajen da aka yi a ofishinta na Kaduna sun nuna cewa waɗannan magunguna ba sa ƙunshe da sinadaran haɗa magani ko kadan, “wanda hakan ke jawo mummunar barazana ga lafiya da ma jawo haɗarin mutuwa.”

Kazalika ta ce an yi wa magungunan rajista da lambobi da adireshin ƙarya. “Tuni an rufe masana’antar haɗa magungunan jabun da ke Tafa a jihar Neja har sai an gudanar da bincike.

NAFDAC ta ce tana jaddada aniyarta ta hana samar da magunguna da kayayyaki na jabu, sannan ta yi kira ga ‘yan ƙsar da su ba da rahoton duk wasu ayyuka na ba daidai ba don taimakawa wajen rage “wannan mummunar halayya daga cikin al’ummarmu.”

TRT Afrika