Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta gargaɗi ‘yan ƙasar dangane da ajiye dafaffen abinci sama da kwana uku a cikin firiji.
Hukumar ta ce ajiye abinci a cikin firji na tsawon kwanaki zai iya sawa ƙwayoyin cuta su gurɓata abincin wanda hakan zai iya jawo rashin lafiyar da za ta iya ajalin mutum.
Jaridar The Nation a Nijeriya ta ruwaito Darakta Janar ta NAFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye na kira ga dukkan masu ruwa da tsaki a harkar samar da abinci da su dauki matakan da suka dace domin tabbatar da ingancin abinci da kuma kawar da duk wata barazana da za ta iya jawo hatsari game da ingancin abinci.
Daraktar ta yi wannan jawabi ne a taron Ranar Kula da Amincin Abinci ta Duniya wadda ke da laƙabin: Amincin Abinci: Ku shirya wa abin da ba ku yi tsammani ma,’ inda ta jaddada cewa amincin abinci ya rataya ne a wuyan kowa.
Ta bayyana cewa akwai rawar da kowa zai iya takawa domin tabbatar da ingancin abinci tun daga masu samar da shi zuwa masu cin sa.
A cewar darakta janar ɗin a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara kan harkokin yada labarai na hukumar, Sayo Akintola ya fitar a ranar Talata, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta kiyasta cewa a duniya, ɗaya daga cikin mutum 10 na fama da rashin lafiya, kuma 420,000 ke mutuwa a kowace shekara saboda cin gurbataccen abinci.