NAFDAC na yawan kai samame wuraren da ake yin jabun magunguna da kayayyakin abinci. / Hoto: NAFDAC

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta gano wasu rukunin shaguna sama da 240 da ake yin lemon kwalba na bogi.

Hukumar ta bayyana haka a wata sanarwa da ta fitar bayan ta kai samame kasuwar Eziukwu da ke Aba a Jihar Abia.

A kasuwar, akwai jerin shaguna daban-daban wadanda ke samar da lemon kwalba nau’i daban-daban ta hanyar satar fasaha da kuma amfani da sinadarai marasa inganci domin kwaikwayon lemon kamfanin na asali.

Hukumar NAFDAC ta bayyana cewa shagunan na yin jabun kayayyaki wadanda suka hada da barasa nau’in Seaman Schnapps da Henessy da Four Cousins da Martell da sauransu.

Haka kuma shagunan suna sauya kwalba da gwangwani ga kayayyakin da suka lalace irin su Coca-Cola da madarar Peak da tumatirin kwalba na ketchup da sauransu.

Hukumar ta bayyana cewa samamen da ta kai ya yi sanadin lalata kwalayen jabun kayayyaki 1,500 wadanda kudinsu ya kai kimanin miliyan 750 da kuma daukar kwalaye 300 zuwa dakunan ajiyar NAFDAC.

NAFDAC ta bayyana cewa ta kama mutum 10 kuma za ta gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike.

TRT Afrika