A lokacin Janar IBB ne aka mayar da Fadar Shugaban Ƙasar Nijeriya zuwa Abuja daga Legas.

Tsohon shugaban mulkin sojin Nijeriya Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya ce ya ɗauki alhakin duk abubunwan da suka faru a lokacin mulkinsa ciki har da soke zaben June 12.

Janar Babangida ya bayyana haka ne ranar Alhamis a Abuja lokacin da yake jawabi wajen ƙaddamar da littafin tarihinsa da ya rubuta.

A yayin da yake tsokaci kan littafiin, tsohon Mataimakin Nijeriya Farfesa Yemi Osibanjo ya karanto wata saɗara da Janar Babangidan ya rubuta wacce ta ce, "Lallai Mashood Abiola shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1993 bayan da ya samu ƙuri'u fiye da miliyan takwas inda ya samu nasara a kan Bashir Othman Tofa na jam'iyyar NRC mai ƙuri'a fiye da miliyan biyar.”

Kazalika da yake jawabi a wajen taron, Janar IBB ya ce daga cikin abubuwan da yake da-na-sanin yi a rayuwarsa har da soke zaɓen na 1993.

Janar Ibrahim Babangida ya shafe shakara takwas a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya, kafin daga baya cece-kuce da tayar da haƙarƙari da aka dinga yi a kan soke zaɓen ya sa ya sauka daga mulki a 1993.

Janar IBB ya miƙa mulkin ga gwamnatin riƙon ƙwarya ta Ernest Shonekan, wanda ɗan garinsu Abiola ne.

Zaben 12 ga Yunin 1993

"Na ɗauki dukkan alhakin abin da ya faru a matsayina na Shugaban Ƙasar NIjeriya a lokacin da wannan abun ya faru," in ji Janar Babangida.

Wannan ne karon farko da yake magana kan wannan batun soke zaɓen da aka yi fiye da shekaru 30 da suka gabata, wanda ya sha jawo cece-kuce a ƙasar.

Tun bayan shekarar 1993 ne wasu masu fafutuka suke bikin tunawa da ranar a duk sanda ta zagayo.

Amma ba a fara yin bikin ranar a hukumance ba sai a 2018 da tsohon shugaban ƙasa Muhamamdu Buhari ya bai wa marigayi Cif Abiola babbar lambar girmamawa ta GCFR a ranar bikin tunawa da ranar zaben 12 ga watan Yunin shekarar 1993, sannan ya ayyana cewa ranar ta koma ita ce Ranar Dimokraɗiyya ta Nijeriya maimakon ranar 29 ga watan Mayu da aka saba.

TRT Afrika