Wani helikwafta ɗauke da mutum takwas ya yi hatsari a jihar Ribas da ke Nijeriya, inda Ma’aikatar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Ƙasar ta tabbatar da mutuwar mutum uku.
Sanarwar da ma’aikatar ta fitar a shafinta na X ta ce jirgin ya faɗa cikin ruwa ne yayin da yake wucewa ta saman yankin Bonny Finima na Tekun Atlantika a ranar Alhamis.
“Mun samu labari marar dadi na hatsarin helikwafta da ya faru ranar 24 ga watan Oktoba da misalin 11:22 na safe a sararin samaniyar tekun Fatakwal.
Jirgin na kamfanin Sikorsky SK76 mai lamba 5NBQ yana kan hanyarsa ne ta zuwa yankin ayyukan man fetur na NUIMANTAN daga sansanin soji na Fatakwal na DNPM,” in ji sanarwar.
Ta ƙara da cewa: “An sanar da Hukumar Binciken Tsaro ta Nijeriya, kuma nan da nan aka fara aiki da kungiyoyin bayar da agajin gaggawa, kuma ana ci gaba da aikin bincike da ceto tare da tallafin Hukumar Bincike da Ceto ta Nijeriya da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Nijeriya (NCAA) da Hukumar Binciken Tsaro ta Kasa (NCAA) da sauran hukumomin da suka dace.
“Sannan an sanar da filayen jiragen sama da ke maƙwabtaka don su taimaka.” “Yayin da ba a samu siginar gaggawa ba (ELT), amma ana ci gaba da kokarin gano inda hatsarin ya afku, kuma an tura duk wani abu da ake da shi, da suka hada da sojoji da jiragen sama masu saukar ungulu don taimakawa wajen ganowa da ceto duk wanda ya tsira. “Ya zuwa yanzu, an gano gawarwaki uku.
“Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo, yana aiki tukuru tare da duk hukumomin da abin ya shafa don tabbatar da yin abin da ya dace da rage asarar rayuka daga wannan mummunan lamari.
"Za a ba da ƙarin bayani yayin da sakamakon bincike ke fitowa. "Tunaninmu da addu'o'inmu suna tare da iyalan wadanda ke cikin jirgin, kuma mun kuduri aniyar bayar da tallafin da ya dace a wannan mawuyacin lokaci."