Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasar Libya ta ce akalla mutum tara ne suka mutu yayin da wasu 16 suka jikkata a ranar Juma’a a yayin arangamar da aka yi tsakanin wasu ƙungiyoyin ‘yan bindiga biyu a Tajoura da ke gabashin birnin Tripoli na kasar Libya.
Duk da haka, hukumar bayar da agajin ba ta fayyace ko waɗanda aka kashen fararen hula ne ko kuma mayaka ba.
Wata majiyar tsaro wadda ta yi magana da kamfanin dillancin labarai na Anadolu bisa sharadin sakaya sunanta, ta bayyana cewa an gwabza fada tsakanin mayakan Rahbat al-Duru da na Al-Shahida Sabriya.
Majiyar ta ce rikicin ya samo asali ne bayan wani yunkurin kashe Bashir Khalafallah, shugaban kungiyar Rahbat al-Duru. Sai dai majiyar ba ta tabbatar da ko su wane ne ke da hannu a yunkurin kashe shi ba.
Kasar Libya dai ta jima tana fama da matsalolin tsaro a dai dai lokacin da ake ci gaba da rarrabuwar kawuna a siyasance tun shekara ta 2022.
A halin yanzu dai ana gudanar da kasar ne a karkashin gwamnatoci guda biyu masu gaba da juna: gwamnatin hadin kan kasa da Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita (GNU) karkashin jagorancin Abdul Hamid Dbeibeh mai hedikwata a birnin Tripoli mai iko da yammacin kasar, da kuma gwamnatin Osama Hammad, wanda gwamnatin kasar ta nada. Majalisar wakilai, wadda ke aiki daga Benghazi kuma tana mulkin yankin gabashi da wasu sassan kudanci.
Kokarin da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta na gudanar da zabukan 'yan majalisa da na shugaban kasa ya ci tura, lamarin da ya kara tsawaita dambarwar siyasar kasar tare da kara ta'azzara yanayin tsaro a kasar mai arzikin man fetur.