Shirin ya ce yana bukatar dala miliyan 185 domin taimaka wa al’ummar da ke Chadi a watanni shida masu zuwa. / Hoto: Reuters

Shirin Samar da Abinci na Majalisar Dinkin Duniya WFP a ranar Talata ya bayyana cewa daga watan Janairu mutum miliyan 1.4 da ke Chadi daga ciki har da sabbin ‘yan gudun hijira da suka tsere daga yankin Darfur na Sudan za su daina samun tallafin abinci sakamakon karancin kudi.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito WFP yana cewa matsalolin kudi da kuma karuwar bukatar agajin jinkai sun tilasta wa Shirin dakatar da bayar da agaji ga wadanda suka rasa muhallansu a Nijeriya da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Kamaru daga watan Disamba.

A wata sanarwa da WFP ya ta fitar, ya tabbatar da cewa daga watan Janairu dakatar da bayar da agajin zai shafi har Chadi.

Sama da ‘yan gudun hijira 540,000 ne suka tsallaka cikin Chadi daga Sudan tun bayan da yaki ya barke tsakanin sojojin Sudan da kuma rundunar RSF kamar yadda Hukumar da ke Kula da ‘Yan gudun Hijira ta Duniya IOM ta tabbatar.

Da yawa sun tsere daga yammacin Darfur, inda rikicin kabilanci da kuma kashe-kashen jama'a suka kara ta’azzara a cikin wannan watan a El Geneina babban birnin jihar, lamarin da ya sa dubban mutane tserewa.

“Lamari ne mai tsoratarwa amma ‘yan Darfur da dama sun gudu zuwa Chadi watanni shida da suka gabata fiye da yadda aka samu a shekaru 20 da suka gabata,” in ji Pierre Honnorat, babban daraktan WFP da ke kasar Chadi.

WFP ya ce a halin yanzu yana bukatar dala miliyan 185 domin taimaka wa al’ummar da ke Chadi a watanni shida masu zuwa.

Reuters