Motar dakon mai da ta ɗaukar shanu ce suka yi taho mu gama. Hoto: Channels TV

Akalla mutum 48 ne suka mutu a ranar Lahadin da ta gabata bayan da wata motar dakon mai ta yi bindiga sakamakon taho mu gama da wata motar mai ɗauke da shanu a Nijeriya, in ji wani jami'i.

“Mutane 48 ne suka mutu,” in ji kakakin gwamnan jihar Neja a wata sanarwa da ya aike wa manema labarai.

Hatsarin ya faru ne a lokacin da wata tanka dauke da man fetur ta yi karo da wata mota dauke da shanu da ‘yan kasuwa a gundumar Angei da ke jihar Neja, kamar yadda Abdullahi Baba Arah, shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Neja ya fada a wata sanarwa da ya fitar.

“An riga an tabbatar da mutuwar mutane sama da 30, sannan shanu masu rai fiye da 50 sun ƙone,” in ji shi.

Ya ce tuni tawagar hukumar ta RRT ta fara gudanar da bincike da mayar da yin abin da ya dace a wurin.

Mai magana da yawun hukumar agajin gaggawa Ibrahim Husseini ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Turkiyya na Anadolu daga wurin da lamarin ya faru cewa ana ci gaba da gudanar da bincike har zuwa yammacin Lahadi.

Gwamnan jihar Neja Mohammed Umaru Bago ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai jajantawa iyalai da al’ummar da suka rasa rayukansu.

AA