A kauyen Ayorou, daya daga cikin wadanda aka yi rikicin, an kashe mutum hudu tare da jikkata mutum 26 da harsasai da wukake, a cewar wata majiya a yankin.

Akalla mutum 28 ne suka rasa rayukansu sakamakon wani rikici da ya barke a wasu kauyuka da ke kudu maso yammacin Nijar a cikin makon nan.

Wani babban jami’i a yankin Tillaberi da ke kusa da Mali ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa “A yanzu mun gano gawarwaki 28, amma watakila adadin ya karu.”

Ya kara da cewa “sai dai ruwan Kogin Neja ya tafi da wasu gawarwakin.”

An fara rikicin a ranar Talata da yamma aka kawo karshensa a ranar Laraba da tsakar rana.

A kauyen Ayorou, daya daga cikin wadanda aka yi rikicin, an kashe mutum hudu tare da jikkata mutum 26 da harsasai da wukake, a cewar wata majiya a yankin.

Sai dai hukumomin mulkin sojan da suka yi wa Shugaba Mohamed Bazoum juyin mulki ba su tabbatar da kashe-kashen ba.

Daya daga cikin majiyoyin ya ce “an kashe fararen-hula kusan100” a rikicin baya-bayan nan a kusa da iyakar Burkina Faso da Mali, inda masu ikirarin jihadi ke yawan kai hare-hare.

Wani fitacce a kungiyar farar-hula ta yankin ya ce rikicin ya samo asali ne sakamakon “yawan hare-haren ramuwar gayya” tsakanin makiyaya na Peul da kabilar Djerma wadanda suke zaune a yankin.

“An kai wa makiyayan hari ne sai matasan kabilarsu suka kai harin ramuwa… sai aka yi ta kai hare-haren ramuwa a kauyukan,” a cewar mamban na kungiyar fararen hula.

Kungiyoyin biyu sun fafata a karshen watan Afrilu da farkon Mayu a kauyukan da suke kusa da kogin inda gomman mutane suka mutu wasu kuma suka jikkata. Dubbai kuma sun rasa matsugunansu.

Wani dan jarida ya shaida wa AFP cewa rikicin Afrilu da Mayun sun biyi bayan “kashe-kashe da dama” na mutanen kauyen da ake zargin masu ikirarin jihadi da yi, wadanda suke sace shanu da karbar haraji.

A lokacin mulkin Shugaban Bazoum hukumomi na yawan wayar da kan al’umma da gargadin mutane da su guji abin da masu ikirarin jihadi ke yin a assasa wutar rikicin kabilanci a tsakaninsu.

AFP